Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Daga ranar 4-5 ga Janairu 1967 wakilan gwamnatin soja ta Nijeriya ƙarƙashin Laftanar Kanar Yakubu Gowon da na ‘yan aware ƙarƙashin gwamnan mulkin soja na jihar kudu maso gabar su ka yi zama a garin Aburi da ke gabashin ƙasar Ghana don kawo maslaha. Dalilin neman maslahar shi ne bayan juyin mulkin soja ranar 15/1/1966 da a ka hakikance ‘yan kabilar Igbo ne su ka shirya har su ka kashe Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello, gwamnan kudu maso yamma Chief Ladoke Akintola; Nijeriya ta shiga zaman zullumi a gwamnatin soja ta farko ta Janar Aguiyi Ironsi. An ruwaito cewa shugaban ƙasa Chief Nnamdi Azikwe wanda Igbo ne, ya riga ya fice ƙetare da sunan neman magani a ƙarshen 1965 kuma an hakkake ya na da labarin juyin mulkin don haka ya kauce. Hakanan su Nzeogwu da su ka harbe Gamji sun bar gwamnan yankin Igbo Dokta Francis Akanu Ibiam sai dai kawai Ironsi ya maye gurbinsa da Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu uban ‘yan aware.
A watan Yuli 1966, dakarun sojoji na Arewa da jagorancin runduna ta Janar Theophilus Yakubu Danjuma ta shiga Badun inda su ka tarar da Janar Ironsi a can kuma hakanan ya kawo ƙarshen rayuwar Ironsi da Laftanar Kanar Adekunle Fajuyi. Ranar 1 ga Agusta 1966 a ka tabbatarwa Janar Yakubu Gowon zama shugaban gwamnatin soja ta Nijeriya.
Ojukwu ne ya zaɓi a tafi Ghana don wannan taro bisa rashin yarda cewa in ya tafi da jama’arsa Lagos ko Kaduna ko Badun zai iya samun matsala. An kammala taro na kwana biyu da damƙa ƙarfin iko na sauye-sauye ƙarƙashin majalisar mulkin soja a Legas ƙarƙashin mai girma babban kwamanda Yakubu Gowon. Mummunar fassarar da Ojukwu ya yi cewa ƙarfin Gowon zai hana shi rawan gaban hantsi ya sa shi ayyana kafa ƙasar Biyafara. Sojojin Nijeriya sun share wata 30 tun daga 1967-1970 don sake haɗe Nijeriya. Janar Olusegun Obasanjo ya jagoranci rundunar ‘yan shigar-sauri su ka kwace Unuohia da hakan ya raba Biyafara gida biyu inda daga bisani su ka sake kwace ƙaramin filin saukar jirage na Uli inda ta nan ne Biyafara ke samun tallafi daga ƙetare. Tun da Ojukwu ya ga dugu-dugu sai ya arce Cote d’iɓoire inda shugaba Feliɗ Boigny da ya amince da Biyafara ya ba shi mafakar siyasa. Ikon Allah sai a 1980 lokacin marigayi Shugaba Shehu Shagari ya hau karaga sai ya yafewa Ojukwu inda ya dawo Nijeriya a ka kyale shi har ma ya shiga siyasa kuma kafin mutuwarsa 2011 ya kafa jam’iyyar APGA.
Mu koma baya, mataimakin Ojukwu, wato Janar Philip Effiong ya mika kansa ga Janar Obasanjo wanda shi kuma ya jagorance shi da burbudin ‘yan Biyafara ya kawo shi gaban Janar Gowon wanda ya karɓi tubansu. Shikenan Nijeriya ta dawo daya har zuwa yau din nan. Janar Gowon ya kafa hukumar ɗalibai masu yi wa kasa hidima NYSC don matasa da su ka kammala jami’a su riƙa zuwa sassa daban da garuruwansu don koyon al’adun sauran ‘yan ƙasa. Hakanan Janar Gowon ya ayyana kammala yaƙi da yafiya cewa ba wanda a ka yi galaba a kansa “no ɓictor nor ɓanƙuished”
Tarihi ya gano makashin Firimiya Sir Ahmadu Bello, wato maciyin amana Chukuwuma Nzeogwu cikin motar yaki da ‘yan tawayen Biyafara. Nzeogwu na cikin mota mai sulke a mafi shaharan kauli daf da Nsukka, sojojin Nijeriya su ka harba ma sa albarushi da hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Duk da laifin da ya tabka na zubar da jini ga shiga yaƙi na wargaza Nijeriya, Janar Gowon ya ba da umurni a dawo da shi mahaifarsa Kaduna a yi ma sa jana’iza ta cikekken babban soja wato taron nan da a kan harba bindigar igwa.
In ban da fitinar su Nzeogwu, Ojukwu da sauran ‘yan awaren Biyafara, Nijeriya na zama kasa daya al’umma daya. Idan a zamanin yau an samu Nnamdi Kanu ya ƙirƙiro sabuwar Biyafara ta neman yaƙin basasa ƙarƙashin IPOB, sai a aza ma sa sunansa na dan tawaye kuma maciyin amanar ƙasa. Kun ga tun da ba soja ba ne, sai ya zabi hanyar farafaganda ta zagin Nijeriya da zuga mutanensa su kashe jami’an tsaro da ‘yan Arewa da ma ‘yan ƙabilar Igbo da su ka barranta da muradin kafa Biyafara. Rundunar ‘yan bindiga ta ESN ta kashe ɗimbin mutane kuma har yau ba ta daddara ba don ma ta mayarda yankin kudu maso gabar mai hatsarin aiki ga jami’an tsaro da zama tarkon mutuwa ga ‘yan Arewa. Yau ka na ɗan Arewa a ka gayyace ka taro a Anacha ai sai ka daure za ka je. Mun ga yanda ziyarar da marigayi Barista Ahmed Gulak ya kai Owerri ta yi sanadiyyar bindige shi a kan titi daga yaran Kanu. Kanu ya na zaman ɗaurin rai da rai daga sassaucin da Jostis Omotosho ya yi ma sa na hukuncin kisa.
IPOB ba ta daddara ba, don ita har kullum ta na ganin sai ta wargaza Arewa kafin samun nasarar dawo da Biyafara. Kai tsaye ma wasu shafukan yanar gizo na ‘yan karyar Hausa zalla na yayata muradin IPOB ne kuma ma’aikacin rediyon Biyafara Chinasa Nworo na shigowa ya na zuga ‘yan Arewa su dau makami su shiga dauki ba daɗi da juna da fakewa da makircin Fulani na kashe Hausawa. Duk wanda bai fahimci kamfen din ba, zai iya dauka abun kirki ne amma hanya ce ta murƙushe dukkan Arewa da kuma yaƙi da musulunci. Duk inda dan ta’adda ya ke, a ma sa hukuncin ta’addancinsa. Logar ɗorawa wata ƙabila laifi ta samo asali ne daga Nnamdi Kanu kuma wai shi ne zai karantar da Hausawa tarihinsu. Wallahi akwai takaici ainun. Dakarun tsaron Nijeriya na bukatar goyon baya don gudanar da aikinsu na kare kasa ciki kuwa da yaki da ‘yan ta’adda. Cikin jami’an nan sojoji da ‘yan sanda za ka iya samun ɗan kowace ƙabila, amma Nijeriya su ke yi wa aiki don haka kare Nijeriya shi ne farko.
Jama’a ku rika lura da kyau kan saƙonnin shafukan karyar Hausa zalla za ku ga ruhin IPOB ƙarara kamar hasken rana. Kalmomi na tada fitina da kira ga zubar da jini shi ne su ke ambatawa. Duk inda ku ka wani ya yi wuf ya rubuta abun da ya ga dama to ɗan baranda ne in ma ba mutanen ba ne kai tsaye ke makircin.
Duk ranar da miyagun nan su ka cije su ka fito, ba sauran farafaganda don wasunsu ko Hausar ma ba su iya ba balle har su zama Hausawan bogi. Jama’a ku yi watsi da su.
IPOB magadan Nzeogwu da Ojuwkwu sun fahimci sai sun yi shigar burtu da sunan Hausawa kafin su iya farraka kan Arewa har ya kai ga ɗan ƙungiyarsu ta shan jini ya hau madafun ikon Aso Rock in ya ga dugu-dugu sai ya nemi a yi zaɓen raba gardama REFERENDUM don kafa Biyafara. Don gudun tsangwama, hatta ‘yan siyasar Igbo masu cin zaɓe su shigo majalisa a Abuja ko samun manyan mukamai, kan mara baya ga Nnamdi Kanu. Duk wanda ya bijirewa Kanu sai dai ya yi ta yawo da dandazon jami’antsaro in kuwa ba haka ba, mayaƙan IPOB wato ESN su bindige shi. Sun kashe mutane da dama sun tarwatsa rumfunan zaɓe sun hana fitowa ranakun Litinin, sun gurgunta ilimin jihohin kudu maso gabar, sun kashe adadi mai yawa na sojoji da ‘yan sanda da kuma musamman Hausawa da fatake da ke zuwa kasuwanci yankunansu. Mugayen mutane ne marar sa son zaman lafiya.
Hatta makiyaya da su ka jefar da sanda su ka ɗau AK 47, a kasar Igbo su ka yi kos na satar mutane. Duk bayanai na nuna ‘yan fashi na kudanci su ka koyawa bijirarrun makiyayan nan sarrafa bindiga. Duk wannan muguntar da zummar wargaza Arewa ne don cimma burin kafa ƙasar Biyafara.
KAMMALAWA
Haƙiƙa kowa ya san mafi yawan masu zaɓe a Arewa na ɗari-ɗarin barin Igbo ya hau karaga don tuna ta’addancin su Nzeogwu kan manyan magabatan yankin. Marigayi tsohon shugaba Buhari ya so shigowa Aso Rock da mataimakin takararsa Chuba Okadigbo a 2003 amma hakan bai yiwu ba duk da farin jininsa. Hakanan Wazirin Adamawa Atiku Abubkar ya so yin hakan da Peter Obi a 2019 amma nan ma ba nasara. Maimakon Igbo su zauna su natsu su tsara siyasarsu da ƙara haɗa kai da Arewa sai kullum zundumawa Hausawa ashar su ke yi da ayyanasu da dolaye da sauran miyagun kalamai. Kai ko Kiristan Arewa bai isa ya shiga coci a kasar Igbo ba don su na ganinsa Malam Banbarakwai kamar ba shi da hurumin zama Kirista. Yanzu masu nazari na IPOB sun gano dabara ta ɗinka rigar Hausawa su boye sunayensu da hotunansu a soshalmidiya da hada kai da baragurbi a ƙananan ƙabilun MIDDLE BELT da makiya Hausawa wato Maguzawa don kunna fitinar ƙabilanci a Arewa. Duk mai yabon Nnamdi Kanu da nuna gara waɗancan mutanen da waɗannan, to ɗan barandan IPOB ne!
Miyagun sun ji haushi ainun don babban ɗan takara daga yankin Igbo wato Peter Obi maimakon ya ci gaba da kamfen dinsa na 2023 a coci, ya sake tsayawa takara a Leba ‘yan OBIDIENTS su zaɓe shi da tunanin tunkuɗo mu su ƙuri’u daga sharrin Hausawan bogi, sai ya yi wuf ya nufi fadar Atiku Abubakar a jam’iyyar ADC. Ai ɗan siyasa ba sakarai ba ne ba ya cinikin biri a sama. Hausawan bogi sun yi iya sharrinsu da kanbama arnanci amma sun kasa yaudarar Musulmi a Arewa. Ko za su kara shekara 1000 ba za su yi nasara ba. Daga mai ɗinkin rigunan Igbo a ƙasashen Larabawa zuwa dan karyar Hausa zalla mai wankin gawa a Turai ko ma masu hidima ga tsoffin Turawa, su nemi sana’a don haƙiƙa wannan hanyar ba mai ɓullewa ba ce. Duk wanda ke da ja, Allah ya kai mu zaɓen 2027 har zuwa malala gashin tinkiya. Matsiyatan jiya ma me su ka taɓuka balle na yau masu buya a salula wai gudun kar a cafke su. Aikin banza kare na gudun layya.
