Shugaban BUA ya ba ‘yan Super Eagles miliyan N700 duk da shan kaye a hannun Moroko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen Attajirin nan kuma Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabi’u, ya tabbatar da cewa zai bayar da kyautar Dala 500,000 ga tawagar ‘yan Super Eagles duk da Nijeriya ta yi waje a gasar kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025.

A ranar Laraba, mai masauƙin baƙi, Moroko ta doke Nijeriya da ci 4 da 2 a zangon buga fenariti bayan an tashi babu ci a tsakanin ɓangarorin biyu a wasan tsawon minti 120 da suka yi.

Rashin nasarar zura ƙwallo a raga daga ‘yan wasa Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi ne ya bai wa ‘Atlas Lions’ na ƙasar damar hayewa zuwa zangon wasan ƙarshe, wanda za a yi a ranar Lahadi.

Da fari, Shugaban na BUA ya yi alƙawarin bai wa Super Eagles ladar Dala 500,000 da ƙarin Dala 50,000 ga kowane ƙwallo da suka samu damar zurawa matuƙar suka doke Moroko.

To amma duk da cewa ‘yan wasan sun gaza cimma nasarar hakan, hamshaƙin attajirin ya sanar da cewa zai cika musu alƙawarin, kamar yadda ya bayyana a wani rubutu ta shafinsa na X a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa, zai yi hakan ne don karramawa da jinjina wa ƙoƙarin ‘yan tawagar, inda ya ce: “Kun fafata da zukatanku, kun bada dukkan abin da za ku iya da kuma nuna bajintarku a filin.”

Ya ƙara da cewa, kaiwa matakin abin a yaba ne da Nijeriya za ta yi alfahari da shi bisa la’akari da ba kowacce ƙasa ba ce ta yi irin ƙoƙarin da tawagar ta yi.

A yanzu dai, Nijeriya za ta mayar da hankali akan neman gurbin matsayi na uku a karawar da za ta yi Egypt, wato Misra a ranar Asabar.

By Babaji