Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haka kuma za ta sabunta wasu kasuwannin a Ɗandume,Jibiya da Mashi da ke jihar domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Dr Salisu Bala zango ya sanar da haka ga manema labarai bayan zaman kammala zaman majalisar zartarwa karkashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da aiwatar da shawarwarin kwamitin da ya binciki makarantu masu zaman kansu (Private Tertiary Institutions) da ke bayar da shedar NCE da Diploma don inganta inganci da ɗaga darajar ilimi a manyan makarantun jihar.
Haka kuma, majalisar ta amince da siyan kayan fara sana’a ga ɗalibai 1,169 da suka kammala shirin koyon sana’a na haɗin guiwa tsakanin hukumar KASEDA da ƙungiyar kanikawa (NATA) domin ƙarfafa wa matasa gwiwa da kuma inganta dogaro da kai.
Majalisar kuma ta tabbatar da bayar da kwangiloli domin kammala gine-ginen da suka rage a sabbin Makarantun na musamman (Special Schools) na Jiƙamshi, Dumurkul da Charanci waɗanda aka fara a ƙarƙashin shirin AGILE amma aikin ya tsaya saboda ƙarancin kuɗi.
Domin ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a ƙauyuka kuwa, majalisar ta tabbatar da bayar da kwangiloli don samar da rijiyoyin burtsatse a ƙananan asibitoci guda 68 da kuma motocin daukar marasa lafiya mai ƙafa uku (tricycle ambulances) 68 ga wasu asibitoci da aka gyara a faɗin ƙananan hukumomi 34 na Jihar.
Majalisar ta kuma tabbatar da bayar da kwangiloli don sayen kayan gyaran taraktoci da motocin aiki a ƙarƙashin shirin inganta aikin noma na Jihar Katsina, domin tabbatar da ingancin kayan aikin.
Haka zalika, majalisar ta amince da shawarwari da hukuncin da ke cikin farar takarda (White Paper) kan rahoton kwamitin tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi 34 na Jihar, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gyara da tsabtace aikin gwamnati a jihar.
An kuma amince da sabunta hanyoyin bada kwangiloli na gwamnati, daga kiran tayin aiki (Tender Invitation) har zuwa amincewar kwangila (Contract Approval) domin ƙara sauri da rage cin hanci da rashawa wajen bada kwangila.
Majalisar ta amince da aiwatar da dokar kiyaye muhalli a dukkan kwangilolin da gwamnati za ta bada (Katsina State Green Public Procurement Executive Order) don inganta muhalli da kuma samar da ayyuka masu inganci.
Dr zango ya ce waɗannan matakai sun ƙara tabbatar da ƙudurin gwamnatin Jihar Katsina wajen samar da kyakkyawan shugabanci, ci gaba mai ɗorewa da bunƙasar tattalin arziki ga al’ummar Jihar Katsina
