Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Nijeriya ta samu matsayi na 72 daga cikin ƙasashe 188 a jadawalin amfani da AI ta ‘2025 Global Government AI Readiness Indeɗ’, wanda ke nuna yadda gwamnatoci ke shirye-shirye wajen amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI a ayyukan gwamnati.
Wannan sakamako ya sanya Nijeriya cikin manyan ƙasashen Afirka ta kudu da Sahara da suka fi nuna ƙwazo a fannin AI.
Rahoton, wanda cibiyar Oɗford Insights ta wallafa, ya yi nazari kan gwamnatoci 195 ta hanyar amfani da ma’auni 69 da aka rarraba zuwa ginshiƙai shida da suka haɗa da ƙarfin manufofi, tsarin shugabanci, gine-ginen fasaha, amfani da AI a sashen gwamnati, bunƙasa da yaɗuwar fasaha, da kuma juriyar tsarin.
A cewar rahoton, Nijeriya ta zo ta huɗu a Afirka ta kudu da Sahara, bayan Kenya wacce ta zo ta 65, Afirka ta Kudu ta 67, da Mauritius ta 71. Wannan ya sanya Nijeriya cikin ƙasashen da suka fi ƙwarewa a nahiyar wajen shirin amfani da AI.
Daga cikin ƙasashen Afirka, goma ne kacal suka samu shiga cikin manyan ƙasashe 100 na duniya, abin da ke nuna cewa nahiyar na samun ci gaba a hankali duk da akwai giɓin ci gaba a wasu wurare.
Rahoton ya bayyana Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi samun matsayi mai kyau a duniya, yana mai nuna cewa matakan manufofi da zuba jari a fannonin fasaha da gwamnati ke yi sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Ko da yake Nijeriya ta zo ta 72 gaba ɗaya, ta fi nuna ƙarfi a wasu bangarori, musamman a ɓangaren ƙirƙira da aiwatar da manufofi inda ta samu matsayi na 35 a duniya, da kuma ɓangaren bunƙasa da yaɗuwar fasaha inda ta samu matsayi na 49. Wannan ya nuna bunƙasar muhalli na AI a ƙasar, ƙaruwa a yawan kwararru da kuma ƙoƙarin gwamnati wajen tsara manufofin AI.
Rahoton ya kuma ambaci buɗe cibiyar Nigeria AI Scaling Hub, wacce ta nuna yadda Nijeriya ke matsawa daga matakin tsara manufofi zuwa aiwatarwa kai tsaye a ayyukan gwamnati.
Sai dai duk da wannan ci gaba, rahoton ya nuna akwai matsaloli da har yanzu ke kawo cikas, ciki har da ƙarancin gine-ginen fasahar AI, ƙarancin amfani da AI a sashen gwamnati, da kuma giɓi a tsarin wutar lantarki da fasahar zamani.
A cewar rahoton, yankin Afirka ta kudu da Sahara gaba ɗaya na matsayi na tara cikin yankuna tara na duniya, da matsakaicin maki 28.04, abin da ke nuna cewa duk da Nijeriya na kan gaba a yankin, har yanzu akwai ƙalubale na tsarin ci gaba.
A wani mataki na ƙarfafa sha’awar AI, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Dijital, Dakta Bosun Tijani, ya sanar da buɗe Cibiyar ƙwarewa ta ƙasa kan AI a Jami’ar Jos a ranar 7 ga Janairu, 2026, yayin bikin yaye ɗalibai na jami’ar karo na 50.
Ministan ya ce, wannan mataki na nuna ƙudirin Nijeriya na rashin zama mai kallo kawai a fannin AI, ko mai karɓar dokoki daga wasu ƙasashe.
“AI yana ginuwa ne kan lambobi, kuma Nijeriya tana da lambobi. Mu ƙasa ce babba da ba za ta tsaya a gefe ba wajen wannan fasaha,” inji Tijani.
Ya ƙara da cewa, jami’o’in Nijeriya su ne ya kamata su jagoranci bincike kan bayanan da suka dace da halin ƙasar, maimakon dogaro da tsarin AI da aka horar da bayanai daga ƙasashen waje.
A ƙarshe, rahoton ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai babbar buri a fannin AI, amma aiwatarwa na tafiya a hankali. Duk da cewa manufofi da bunƙasa tsarin fasaha na inganta, ƙarancin amfani da AI a ayyukan gwamnati har yanzu babbar giɓin da ke buƙatar gyara ne.
Rahoton ya yi hasashen cewa ikon Nijeriya wajen sauya manufofi zuwa aiki a zahiri shi ne zai tantance ko za ta iya hawa sama a jadawalin duniya na shirye-shiryen AI a nan gaba.
