Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata babbar kotu da take zamanta a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, ta rufe ƙarar ɓata suna da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Udughan. Alƙalin kotun, Mai-shari’a Chizoba Orji, ta yanke hukuncin ne bayan lauyan gwamnati, Aderonke Imana, ta shigar da buƙatar janye ƙarar.
Bayan haka, lauyan Sanata Natasha, West Idahosa, ya roƙi kotu da ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya bisa wannan mataki na gwamnati. Idahosa ya kuma buƙaci kotu da ta umarci a mayar da dukkan takardun da aka karɓa daga hannun Sanata Natasha da masu tsaya mata a shari’ar, kamar fasfo ɗin sanatar da makamantansu. Lauyar gwamnati ba ta nuna wata adawa ba kan wannan buƙata ba.
A cikin gajeren hukunci da ta yanke, Alƙali Orji ta yi watsi da ƙarar gabaɗaya tare da sallamar masu tsaya wa Sanata Natasha, ta kuma bayar da umarni da a mayar musu da dukkan takardunsu da aka karɓa a lokacin shari’ar.
Gwamnatin Tarayya ta shigar da wannan ƙara ne a watan Mayun 2025 bisa zargin cewa, Sanata Natasha ta yi kalaman ɓata suna a wata hira da ta yi kai tsaye a gidan talabijin. An shigar da ƙarar ne a ranar 16 ga Mayu, 2025, inda aka sanya sunan Akpoti-Udughan a matsayin wacce ake ƙara kai tsaye.
Gwamnatin ta zargi Sanatar da karya sashe na 391 na Dokar Penal Code, inda ta ce ta yi zargin da ta san zai ɓata sunan wasu mutane ko kuma ta yi hakan ne tana da dalilin zaton hakan zai cutar da martabarsu. Laifin yana da hukunci ƙarƙashin sashe na 392 na wannan doka.
ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen ya danganci zargin da Sanata Natasha ta yi cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, sun shirya kashe ta. A cikin hirar talabijin ɗin, Sanatar ta ce an tattauna batun kashe ta ne a wata ganawa da Akpabio ya yi da Bello.
Ta kuma ce janye mata jami’an tsaro da aka yi ya sanya ta cikin hatsari, tana mai cewa hakan wata dabara ce ta sa a kai mata hari. Gwamnatin Tarayya ta ce Sanatar ta san ko ta kamata ta sani cewa irin waɗannan kalamai za su bata sunan Shugaban Majalisar Dattawa.
Duk da haka, da janye ƙarar da gwamnatin ta yi, kotu ta yanke hukuncin sallamar dukkan bangarorin, lamarin da ya kawo karshen shari’ar.
