Rikicin tsige gwamnan Ribas ya fara taɓarɓarewa bayan majalisa ta kasa zama

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Dokokin Jihar Ribas, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Martin Amaewhule, ta kasa komawa zaman majalisa a ranar Alhamis kamar yadda aka tsara, abin da ya ƙara jefa shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, cikin ruɗani.

A zaman farko na shekarar 2026 da majalisar ta yi a makon jiya, ‘yan majalisar sun ƙaddamar da shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa bisa zargin aikata manyan laifuka a mulki.

Daga cikin tuhumar da aka yi musu akwai rusa ginin Majalisar Dokokin Jihar Ribas, zargin kashe kuɗaɗen gwamnati ba tare da amincewar majalisa ba, da kuma wasu matakai da aka ce an ɗauke su ba tare da sahalewar majalisar ba.

A ƙarshen wancan zama, majalisar ta ɗage zaman zuwa ranar Alhamis, 15 ga watan Janairu, 2026, inda ake sa ran za a ci gaba da tattaunawa kan shirin tsige gwamnan. Sai dai zuwa ƙarfe 12 na rana a wannan Alhamis, babu alamun wani shiri na zaman.

Tun bayan rusa babban ginin majalisar, ‘yan majalisar ke gudanar da zamansu a ɗakin taro da ke cikin gidajen zamansu na hukuma a titin Aba, a birnin Fatakwal. Duk da cewa ranar ta kasance rana da aka sanya domin komawa zama, wajen ya kasance kango, ba tare da wata alama da ke nuna cewa majalisar za ta zauna ba.

Zuwa yanzu, shugabancin majalisar bai fitar da wani bayani ba dangane da dalilin da ya sa aka kasa zama, haka kuma ba a sanar da wata sabuwar ranar komawa zaman ba. ƙoƙarin jin ta bakin shugaban kwamitin majalisa kan yaɗa labarai, koke-koke da ƙararraki, Eneme George, ya ci tura, domin wayoyinsa ba su amsa ba, saƙonnin da aka tura masa ma ba a samu amsa ba.

Halin da ake ciki ya sa makomar shirin tsige gwamnan ta kasance cikin duhu, yayin da idanu ke kan shugabannin majalisar domin ganin matakin da za su ɗauka a gaba.

By ukarofi