
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, wato Abba Abubakar, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC mai mulki, yana mai bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar da haka a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda wasu jagororin APC daga yankin Arewa ta Gabas suka tarbe shi bisa girmamawa, ranar Alhamis.
Da yake jawabi a taron, Abba ya sanar da yin murabus daga PDP da kuma shelanta matakinsa na komawa APC, hukuncin da ya zama ginshiƙin sabunta alƙiblar siyasarsa.
Haka kuma ya umarci masu taimaka masa a siyasa na ƙungiyar Haske Atiku da aka samar a 2022 da su gaggauta shiga APC tare da shirya fagen goyon bayan ajandar Shugaba Tinubu ta Sabunta Fata.
“Da wannan ci-gaba, zan yi aiki tare da Sanata Barau domin cimma nasarar sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027”, inji shi.
A jawabinsa, mataimakin shugaban APC na Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya bayyana matakin a matsayin abin alfahari musamman duba da yadda jam’iyyar ke ƙoƙari wajen yin siyasar damawa da ɓangarori daban-daban.
Shi ma Sanata Barau a nasa ɓangaren, ya taya Abba murna akan matakin nasa, wanda aka gina bisa tsari da ƙwarewa, yana mai tabbatar masa da samun goyon bayan jagorancin APC.
