
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin tsaro na fararen hula masu goyon bayan sulhu a Jihar Katsina, Kwamared Shamsuddeen Salisu Na Alhaji ya bayyana haka a hira da manema labarai a ɗakin taro ta ƙungiyar ‘yan jarida a Katsina.
Ya ce, sun goyi bayan kokarin da gwamnatin jihar Katsina da al’ummar jihar sukayi,wajan shawo kan matsala tsaro ta amfani da hanyoyi. tattaunawa da yan bindiga..
Kwamared Na Alhaji ya bayyana cewa sun ɗauki wannan matsaya ne bayan nazari da sukayi ta hanyoyi da dama da suka haɗa da tattaunawa da mutanen da ke zaune a kananan hukumomin da ke fama da rashin tsaro.
Ya bayyana cewa, suna sauraron rahotanni na kafafen yaɗa labarai ke bayarwa kan abinda ya shafi tsaro a yankunan kuma sun gano cewa sulhu da al’umma suka ƙulla da yan bindiga na haifar da ɗa mai ido.
A cewarsa, hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane ya rabu da kashi casa’in” Yau mutum zai iya zuwa Batsari ko Jibiya a kowane lokaci koda talatin dare ne ba tare da fargaba ba”, inji Shamsuddeen.
“Manoma sun koma gona,An bude makarantu,An buɗe kasuwanni wanda hakan ya nuna sulhu ya fara maido da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin al’umma,”kwamred Shamsuddeen ya fadi haka.
Ya bayyana cewa Hanyar da aka bi na tattaunawa da yan bindiga a waɗannan yankuna ya magance matsalar da bindiga da jiragen yaki suka gaza magancewa.
Saboda haka shugaban gamayyar kungiyoyin ya ce basu yadda da masu adawa da sulhu ba,”saboda hatta addinin mu ya amince da yin sulhu,”Ya ce.
Haka kuma a yunkurin kudirin gwamnatin jihar Katsina na neman sakin Yan bindiga da ke gida kaso ,ya ce matsayar gamaiyar kungiyoyin shine suna goyon bayan haka Indai matakin zai kawo zaman lafiya a jihar.
Kwamred Shamsuddeen ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohin arewacin kasar da kara baiwa amfani da hanyoyin sulhu wajan fuskantar shawo kan ta’addanci da rikice rikice a yankin Arewa da kasa baki ɗaya.
Gamayyar kungiyoyin sun yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa akan ƙoƙarin da yake yi wajan samar da tsaro da zaman lafiya a faɗin jihar.
