*Shekaru 538 da kafuwar masana’antar rinin ƙofar Mata
Daga IBRAHIM HAMISU da ABDULMUMIN GIWA a Kano
Sana’ar rini, kamar sauran sana’o’i a Nijeriya, musamman a fannin waɗanda aka samar daga masaƙa, suna fuskankar ƙalubale sakamakon durƙushewar tattalin arzikin duniya ko abin da ake kallon sakaci daga ɓangarorin da abin ya shafa. Wannan sakaci ya kai ga durƙusar wata sana’a da a da ta zama ginshiƙin biyan buƙatun tufafi na jama’a daga ƙasashe irin su Mali da Libiya, har ta kusa zama inuwa ko ginshiƙi ta abin da take a baya. Sai dai a baya-bayan nan, Gwamnatin Jihar Kano ta sake waiwayar wannan sana’a da nufin ƙarfafa masu ruwa da tsaki a cikinta. Ta cikin wannan rahoto na musamman da Wakilan Blueprint Manhaja, IBRAHIM HAMISU da ABDULMUMIN GIWA, suka tattara mana, masu karatu za ku fahimci irin muhimmancin da wannan sana’a ke da shi, tarihinta, bunƙasarta da kuma irin yadda take taimaka wa al’umma da kuma tattalin arziki:
Sana’ar rinin auduga a Kano, wacce ake amfani da ita ta hanyoyin gargajiya, sana’a ce da aka fara tun tsawon ƙarnuka kuma ta shahara a yankin Yammacin Afirka. Sana’a ce da ake amfani a tsarin fasaha wajen sauya kamanni ko yanayin kayan sawa irinsu shaddodi wagambari da duk kayan da aka samar daga masaƙa daga auduga.
Rahotanni sun nuna cewa, ramukan rini na Kano da ke ƙofar Mata a cikin birnin Kano a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, sun wanzu tun shekarar 1498 – kimanin ƙarni biyar da suka gabata – kuma ana kallon su a matsayin ɗaya daga cikin mafi tsufa a Yammacin Afirka.
Bincike ya nuna cewa, waɗannan ramuka sun kasance ginshiƙi a bunƙasar kasuwancin kayan mawaka a yankin, inda ake amfani da rini na shuni na gargajiya tare da dabaru da aka gada daga kaka da kakanni. Saboda haka, wannan wani babbar gadon tarihi ce da ake adanawa daga zamani zuwa zamani, kana kuma tana zama abin jan hankali ga baƙi da ke son ganin yadda ake sarrafa tufafi ana rina su ta hanyoyin gargajiya na gida.
Duk da shigowar fasaha da sauye-sauyen tattalin arziki da suka samar wa masu saye da dama na kayan makaƙu na sana’ar rinin auduga ta ci gaba da wanzuwa da gudana, duk da cewa wasu na ganin kamar ta kusa ɓacewa. Dalilin wannan ra’ayi shi ne yawaitar shigowar da tufafin da aka riga aka rina daga ƙasashe irin su China, Indiya da sauran ƙasashe da suka ci gaba. A da, ana cewa wannan sana’a ta samar da ayyukan yi ga dubban mutane, amma a yau, sakamakon raguwar buƙata, yawan masu sayen kaya ya ragu.
Sai dai a wata faɗar ta akasin haka na cewa yawan jama’ar jihar da ƙasar baki ɗaya ya ƙaru matuƙa, inda yawan al’ummar Kano ya kai kusan miliyan 20 idan aka kwatanta da lokacin da sana’ar ke ƙololuwarta. Don haka, abin da ake samarwa a yanzu bai wadatar da wannan yawan jama’a ba.
Wannan bunƙasar yawan jama’a ta zo ne tare da ci gaban fasaha a fannin samar da tufafin yin rini a duniya baki ɗaya, amma duk da haka, wannan sana’a mai shekaru fiye da 500 har yanzu tana nan daram, tare da ƙara yawan masu shiga cikinta. Saboda haka, ba za a ce sana’ar na dab da ɓacewa ba; illa dai kawai an samu yalwar wasu kalolin shaddodi da yaduka. Sana’a ce da ta tsira daga yaƙe-yaƙe, mulkin mallaka da kuma tasirin dunƙulewar tattalin arzikin duniya wato (globalisation), kuma har yanzu tana wanzuwa.
Tarihin wannan sana’ar rini a Kano ba zai cika ba tare da ambaton ’yan kasuwa daga birnin Timbuktu na ƙasar Mali da Tripoli na Libya da ma sauran wurare ba, waɗanda suka riƙa kawo zinariya, gishiri da hauren giwa, yayin da ita kuma Kano ke ba da yaduddukan da aka rina da shuni, waɗanda suka shahara da kwari da kyan gani a lokacin kasuwancin sahara.
Cibiyar ta ƙofar Mata, inda ake samar da kayayyakin, tana nan wajen katangar tsohuwar birnin Kano. Sana’ar ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasa ƙarfi (GDP) musamman bayan samun ’yancin kai, inda mashahuriyar kamfanin sarrafa Auduga ta Gaskiya Mills da ke ɗaukar ma’aikata kusan 300,000 a wancan lokacin.
Waɗannan kayayyakin na idan an rina ana sanya wa sarakuna da masu mulki, kana a wasu lokuta da dama ana amfani da su wajen kawata dawaki. A zahiri, kayayyakin rini su ne suka mamaye kasuwar kayan ado ta zamani a wancan lokaci.
Kafin a rina shadda, wagambari da yadudduka, ana wanke su, ana tsabtace su sannan a ɗaure su da zaren raffia ko auduga cikin salo daban-daban. Wadannan salo ne ke haifar da kala iri-iri na kayan da aka rina, inda ake samun kyawawan zane-zane farare a kan shuɗin bango da makamancin sa.
Tarihin sana’ar:
Wannan tsohuwar sana’a da ke ƙofar Mata a tsohon birnin Kano, an kafa ta ne shekaru 538 da suka gabata ta hannun wani Malam Tabosa, wanda ya zo Kano daga Senegal. A ziyarar gani da ido da na kai wurin ya nuna cewa masu gudanar da sana’ar ‘ya ‘yan gado ne da suka karɓi sana’ar daga iyayensu, kuma suna alfahari da ita, duk da cewa an yi imanin ta ragu daga yadda ta take a baya sakamakon ci gaba. Har yanzu akwai ramin rini na farko da aka fara haƙawa a tarihin sana’ar, kuma ana ci gaba da amfani da shi.
A baya, ramukan rini sun bazu a wurare da dama har da babban titin ƙofar Mata, amma da yawa daga cikinsu an rufe su domin gina hanyoyi. A halin yanzu, an killace wurin tare da ingantawa ginin, inda ake da kimanin ramuka 104.
Yadda ake shirya ramin rini:
Da farko, ana haƙa ramin rini gwargwadon girman da ake buƙata, sannan a cika shi da ruwa. Bayan haka, ana zuba ƙurar toka gwargwado, sannan a sanya wata itaciya mai suna itacen baba. Ana barin sa tsawon kwanaki bakwai, daga bisani a ƙara wani sinadari mai suna katsi tare da amfani da sandar tuƙi wajen gaurayawa. Bayan wasu kwanaki bakwai, ana cire itacen baba bayan ya narke, sannan a ƙara shuni a gauraya, a sake barinsa na kwana biyu.
Sabon rami ana fara gwada shi ne da ɗan kaya kaɗan har sai ya kai yadda ake so. A hankali, ana ƙara yawan yaduddukan da ake rina, duk da cewa ƙarfinsa na rini kan ragu bayan kusan watanni biyar. Duk da haka, ana ci gaba da amfani da shi yayin da ake haƙa wani sabon rami a kusa da shi domin amfani na gaba.
Kafin rami ya zama fara amfani da shi, ana buƙatar akalla makonni biyu. Haka kuma, ramin rini na iya “yin samun matsala,” wanda shi ya sa ake buƙatar kulawar ƙwararru. Wannan na faruwa sakamakon yawan amfani da wasu sinadarai. Masana ne ke gano matsalar tare da bayar da maganin da ya dace, wani lokaci har da amfani da dorawa domin farfaɗo da ramin.
Ana ƙiyasta cewa rami guda na iya rina yadi tsakanin yadi 80 zuwa 100 duk bayan kwanaki biyar, yayin da ake barinsa ya huta sauran kwanakin mako.
Bunƙasar tattalin arziki:
Baya ga kasancewar ta abar yawon buɗe ido, sana’ar rini na da gagarumar gudunmawa ga tattalin arzikin jihar, idan aka kula da ita yadda ya kamata. Wani ƙwararre a sana’ar, Musa Yusuf Dakta, ya bayyana cewa sana’ar rini da suka gada daga iyayensu sana’a ce mai riba sosai. Ya ce ya samu damar gina gida, ya yi aure da sayen mota, tare da ciyar da iyalinsa daga ribar sana’ar. Sai dai ya amince cewa suna fuskantar ƙalubale daga wasu kwastomomi, amma manufarsu ita ce “kwastoma kullum yana da gaskiya.”
Tallafin gwamnati:
Bincike ya nuna cewa tallafin da gwamnati ke bai wa sana’ar ya fi karkata ne ga kiyaye matsayin gadon tarihi da yawon buɗe ido, ba wai bunƙasa ta ko zamanantar da ita ba. A ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, an gyara tare da ƙawata wurin gabaɗaya, inda aka sanya wutar lantarki ta hasken rana da shimfiɗa tayil a kewayen ramuka, duk kyauta daga gwamnati. A wannan cibiya kaɗai, akwai kimanin mutane 70 da ke dogaro da sana’ar, tare da wasu ma’aikatan waje kusan 30. Sana’ar na kuma bayar da damar koyon aiki ga masu sha’awa tare da haɗa hanyoyin rini na zamani.
Kammalawa:
A bayyane yake cewa, ɗorewar masana’antar rini a Kano na da alaƙa ta kai-tsaye da burin bunƙasa tattalin arziki da kare al’adu. Idan gwamnati ta ƙara bai wa sana’ar kulawa, sana’ar za ta rayu; idan aka yi sakaci kuwa, za ta riƙa dusashewa a hankali a hankali. Shigar gwamnatocin jiha da ta tarayya ta hanyar tallafa wa yawon buɗe ido, bunƙasa kasuwancin sana’ar ta hanyar kasuwancin intanet da shirin koyon sana’a, zai ƙara wa jihar Kano da al’ummarta alheri mai yawa.
