
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tauraruwar Super Falcons ta Nijeriya, Asisat Oshoala, ta bayyana fushinta game da abin da ta kira da “bunƙasar mamayar Moroko da mu’amalanta ta musamman”, lamarin da ya sa ta jefa ƙalubale ga shugabancin hukumar kula da lamuran ƙwallon ta Afirka (CAF), tana mai tirjewa akan Nijeriya ce ta fi cancanta ta karɓi baƙuncin gasar AFCON.
Kalaman nata na zuwa ne jim-kaɗan bayan doke Super Eagles a wasan dab da na ƙarshe a gasar ta kofin ƙasashen Nahiyar Afirka da Moroko ta yi a ranar Laraba a zangon buga fenariti.
Asisat, wadda gwarzuwar Afirka ce har sau shida, ta yi zargin naɗa ɗan Ghana, wato Daniel Laryea a matsayin alƙalin wasa ya taimaka wajen faɗuwar ‘yan Super Eagles a wasan, wanda aka gudanar a birnin Rabat na Moroko.
Tun gabanin wasan Oshoala ta nuna damuwa akan karawar, inda ta yi gargaɗin Moroko ka iya amfani da wasu damarmakin da ba sa ƙarƙashin doka wajen samun nasara.
Bayan shan kayen Nijeriya ne sai ta azalzala sokan nata, lamarin da ya sa ta zargi CAF da rashin adalci wajen yi wa mai masauƙin baƙin alfarma.
Daga shekarar 2023 zuwa yanzu Moroko ta karɓi baƙuncin gasa na CAF da dama ciki har da U-23 AFCON, U-17 AFCON, tarukan karrama ‘yan wasa na CAF da kuma AFCON 2025 da ke gudana.
