‘Yan siyasa su guji yin maganganu na tozartawa da cin mutuncin mutane – Danpass

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano 

Dan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya yi kira ga matasa musamman ‘yan siyasa akan su kyautata tarbiyya su guji yin maganganu na tozartawa ko cin mutuncin mutane saboda adawa ta siyasa.

Ya ce abin takaici da yake faruwa a  gidajen rediyo da kafafen sada zumunta sai ka ji matasa suna ta maganganu marasa daɗin ji ga mutane masu kima da yawan shekaru wasu ma sun yi sa a da iyayensu.

Ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya ɗoru akan cin mutunci da tozarta mutane basa gamawa lafiya ko a baya ma a siyasun da suka gabata a ƙasarnan a lokacin babu ma gidajen rediyo kamar yanzu duk masu hawa duro suna yin zage-zage da sharri basu gama lafiya ba.

Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya ce don haka suke tausayawa matasa masu irin wannan hali na cin mutuncin mutane yana gargaɗin su akan su je su duba tarihin na baya suga ya ya suka ƙare a rayuwarsu domin ya zame musu darasi. 

Ya ce ita hamayya ta siyasa ba sai ka ci mutuncin wani ko ka tozartashi ba akwai abubuwa da zaka yi masa na gyara kayan ka musamman ma idan mai mulki ne cikin ladabi da girmamawa da shi kansa in ya ji yasan kazo da abu mai kyau.

Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya yi nuni da cewa duk irin abubuwan da suke faruwa na danbarwar siyasa musamman a Arewa rashin haɗin kai ne ya kawo shi da zamu haɗa kai a tunkari matsalolin dake damun mu ba tare da la’akari da bambanci ba da an yi maganin matsaloli da yawa.

By ukarofi