Gwamna Abba ya cika sama da kashi 80 na alƙawuran da ya yi wa Kanawa – Dr. Nana Asma’u

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Daraktar Bincike da Adana Bayanai ta Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Dr. Nana Asma’u Jibrin, ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samu nasarar cika sama da kashi 80 cikin 100 na alƙawuran da ya yi wa al’ummar Kano a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, cikin shekaru biyu na mulkinsa.

Dr. Nana Asma’u ta bayyana cewa an cimma wannan nasara ne musamman ta fuskar ilimi, lafiya, samar da ayyukan yi, bunƙasa harkar noma, biyan tsofaffin ma’aikata haƙƙoƙinsu na giratuti da fansho, inganta hanyoyin sufuri a birane da ƙauyuka, samar da ruwan sha, da kuma ƙarfafa matasa maza da mata ta fuskar aikin yi.

Ta ƙara da cewa ma’aikatan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba amanar aiwatar da manufofin gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa Kano da Kanawa sun kai matakin cigaba mai ɗorewa, musamman ta fuskar tsaro, zaman lafiya da kwanciyar hankali a zangon farko na mulkinsa. Ta nuna kyakkyawan fata cewa gwamnan zai ci gaba da jan ragamar jagoranci cikin nasara sakamakon goyon baya da ƙaunar da al’ummar jihar ke nuna masa.

Tun da farko, Dr. Nana Asma’u ta nuna farin cikinta kan farfaɗo da makarantu 24 na koyar da sana’o’i da aka gina tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015 a zamanin tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Ta bayyana cewa daga cikin waɗannan makarantu, a makon nan an yaye ɗalibai 2,260 da aka horar da su sana’o’i daban-daban kamar aikin jarida, fasahar kwamfuta (ICT), rainon tsirrai, kiwon kaji, kiwon kifi da kiwon dabbobi, inda aka bai wa kowa kayan aiki domin dogaro da kai da taimakawa al’umma.

By ukarofi