Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Daya daga cikin fitattun jikokin Sheikh Ibrahim RTA kuma Shugaban ƙungiyar Majama’u ta ƙasa, Sheikh Ahmed Tijjani Sani Auwalu, ya bayyana cewa Tijjanawa da masu kishin ilimi a faɗin Nijeriya sun nuna matuƙar farin ciki kan girmamawar da Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci na duniya, marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ta hanyar sanya sunansa a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Azare, Jihar Bauchi.
Sheikh Tijjani Sani Auwalu, wanda kuma shi ne Kwamishinan Al’amuran Addini na Jihar Kano, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai jim kaɗan bayan ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar Majama’ul Ahbab (Sheikh Ibrahim Inyass Association of Nigeria), reshen Jihar Kano, wanda aka gudanar a makon da ya gabata a birnin Kano.
Ya ce wannan mataki ya faranta wa al’umma rai ƙwarai, musamman mabiya ɗariƙar Tijjaniyya a faɗin ƙasar nan, inda ya bayyana girmamawar a matsayin nuna daraja ga gudummawar da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya bayar wajen yaɗa addini, ilimi da zaman lafiya. Saboda haka, Tijjanawa sun yaba wa Shugaban ƙasa kan wannan karamci da ya yi wa “ubanmu”, tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙansa.
A ƙarshe, Sheikh Tijjani Sani Auwalu ya bayyana cewa ƙungiyar Majama’u ƙungiya ce da ke mai da hankali kan shirya Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass a duk shekara, da ayyukan da’awa, yaɗa ilimi, da wayar da kan al’umma kan muhimmancin sana’o’i domin dogaro da kai, a matsayin ginshiƙin bunƙasa tattalin arziki, tsaro da zaman lafiya.
