Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla sababbin ma’aikata 60 da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗauka aiki sun koka, suna zargin bankin da jinkirta tura su bakin aiki tsawon kusan watanni 28 bayan karɓar takardun ɗaukar aiki a hukumance.
Waɗannan mutane, da aka ba su takardar ɗaukar aiki tun watan Agustan 2023, sun ce ba su san ina rayuwar su ta dosa ba bayan sun amince da aikin tare da yin murabus daga wuraren aikinsu na baya kamar yadda CBN ya umarta.
Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, ɗaya daga cikin su, Emmanuel Linus Dabo, wanda ya yi magana a madadin tawagar, ya ce bayan bankin ya ba su tayin aiki, sashen kula da ma’aikata (HR) ya ba su umarni a sarari da suka haɗa da miƙa wa bankin takardar karɓar aiki da kuma shaidar yin murabus daga tsoffin wuraren aikinsu.
“Dukkanmu mun miƙa takardun murabus ga tsoffin masu ɗaukar aikinmu domin mu ci gaba da tsarin CBN,” inji Dabo.
Ya bayyana cewa tsarin ɗaukar aikin ya fara ne tun watan Afrilun 2023 lokacin da suka miƙa takardun Cɓ zuwa hedikwatar CBN. Daga nan sai aka gayyace su ta email domin halartar gwaje-gwajen tantancewa da kuma masa tambayoyi.
Ya ce waɗanda aka tantance sun kuma wuce gwajin lafiya a asibitin CBN, inda aka ba su lambobin sirri kafin a tura su asibitocin waje domin kammala duba lafiyar.
“Bayan amsa tambayoyi, gwaje-gwajen lafiya da na kwakwalwa, HR ta tuntuɓe mu domin mu zo hedikwatar CBN a Abuja mu karbi takardun tayin aiki. Mun cike takardun karɓar aiki muka mayar ba tare da jinkiri ba,” inji shi.
Dabo ya ƙara da cewa, daga baya sashen HR ya sake aiko musu da saƙonnin email inda ya buƙaci su tura dukkan takardunsu domin rajista ta yanar gizo, ciki har da takardar murabus da tsoffin ma’aikata suka amince da ita.
Sai dai bayan sun cika dukkan sharuɗɗan, sun ce bankin ya daina tuntuɓar su gaba daya.
“Bayan dogon lokaci, ba mu ji komai daga bankin ba. Da yawa daga cikinmu mun zama marasa aiki, amma muna ci gaba da jira da fatan za a kira mu. Mun ɗauka canjin shugabanci a CBN ne ya kawo tsaiko,” inji Dabo.
Takardun aka gani sun nuna cewa tayin aikin da aka ba su na wucin gadi ne, tare da sharaɗin gwajin aiki na shekara guda kafin a tabbatar da su idan sun nuna ƙwarewa.
ƙungiyar ta kuma nuna kwafen wasiƙun tunatarwa da suka rubuta wa gwamnan CBN a watan Satumba 2023, Nuwamba 2024 da Janairu 2025, amma sun ce babu wanda aka amsa daga ɓangaren bankin.
Yayin da matsin tattalin arziki ke ƙara tsananta a ƙasar, waɗannan ma’aikata sun ce jinkirin ya yi matuƙar shafar rayuwarsu ta kuɗi da ta zamantakewa.
Sun roƙi Gwamnan CBN, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin magance halin da suke ciki.
“Yanzu haka da yawa daga cikinmu na fama da damuwa ta zuciya. Kwanan nan mun tara naira 3,000 kowannenmu domin taimaka wa wasu da ke kwance a asibiti,” inji Dabo.
“Wasu ba su iya biyan kuɗin haya ko kuɗaɗen buƙatun yau da kullum. Wasu ma sun cire ’ya’yansu daga makaranta saboda sun kasa ɗaukar nauyi. Ba mu san yadda za mu bayyana wannan hali ga iyalanmu ba.”
Ya ƙara da cewa, wasu daga cikin su sun yi karatu a ƙasashen waje, suka dawo gida ne da fatan ba da gudunmawa ga ci gaban ƙasa, amma yanzu sun tsinci kansu cikin halin ƙaƙanikayi.
“Mun dawo gida da kishin ƙasa da fata. Muna roƙon hukumomi da su dubi wannan batu cikin gaggawa, domin halin na ƙara muni kullum,” inji shi.
Zuwa yanzu, Babban Bankin Nijeriya bai fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan ƙorafi ba.
