Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani dillalin sayar da wayar salula a birnin Tripoli na ƙasar Libya ya karɓi wayoyin Nokia da ya yi oda tun a shekarar 2010, bayan shafe tsawon shekaru 16 yana jiran isowarsu.
Lamarin ya janyo hankalin jama’a a shafukan sada zumunta, bayan wani bidiyo da aka yaɗa ya nuna lokacin da aka miƙa masa kayayyakin da ya daɗe yana jira.
A cewar dillalin da abokansa da suka bayyana a bidiyon, an miƙa kayan ga wani wakili a cikin birnin Tripoli tun a 2010, amma duk da cewa mai aikawa da wanda zai karɓa suna zaune a yankin da ke kusa da juna, wayoyin ba su taɓa kaiwa hannunsa ba tsawon waɗannan shekaru.
A cikin bidiyon, dillalin na dariya tare da abokansa, yana cewa cikin barkwanci, “Wazannan wayoyi ne ko kayan tarihi?” kalaman da ke nuna yadda fasahar wayar salula ta sauya matuƙa tun daga wancan lokaci.
Rahotanni sun nuna cewa yaƙin basasar Libya na shekarar 2011, da rugujewar tsarin sufuri da na kwastom, ne suka sa kayan suka maƙale a rumbunan ajiya tsawon sama da shekaru goma.
Har yanzu ƙasar na fama da rabuwar kai tsakanin gwamnatoci biyu – ɗaya a Tripoli, ɗaya kuma a gabashin ƙasar – lamarin da ke ci gaba da durƙusar da hanyoyin kasuwanci da jigilar kaya tun bayan kifar da tsohon shugaba Muammar Gaddafi.
Lokacin da aka buɗe akwatunan a shekarar 2026, an tarar da tarin tsofaffin wayoyin Nokia masu maballi, irin waɗannan da aka daɗe ba a amfani da su a wannan zamani na wayoyin zamani. Wayoyin sun zama tamkar kayan tarihin fasahar sadarwa.
Yayin da mutane da dama suka ɗauki lamarin da dariya, wasu sun bayyana cewa jinkirin isowar kayan na nuna irin tasirin da yaƙi ke yi wajen durƙusar da kasuwanci da hanyoyin safarar kaya. Wasu kuma sun yi nuni da cewa wayoyin na iya zama masu daraja a yanzu a matsayin kayan tarin tarihi, ganin yadda tsofaffin wayoyin Nokia ke samun karɓuwa a matsayin kayayyakin ado ko tarihin fasaha.
