Daga ABDULLAHI MUHAMMAD, Katsina
Cibiyar Horas da Matasa Sana’o’i ta KYCV mallakar Gwamnatin Jihar Katsina ta kammala gyara da sabunta motocin gwamnati guda tara, matakin da ke nuna jajircewar gwamnati wajen kula da kadarorin gwamnati da kuma rage asarar kuɗi.
Shugaban cibiyar, Injiniya Kabir Abdullahi Kofar Soro, ya bayyana wa manema labarai cewa nasarar aikin ta ƙara tabbatar da ƙudurin gwamnatin jihar na inganta amfani da kadarorin gwamnati cikin tsari mai inganci tare da tanadin kuɗi.
A cewarsa, motoci ƙirar Toyota Hiluɗ guda biyu sun samu cikakken gyara da sabuntawa, inda aka daidaita su yadda za su ci gaba da aiki cikin inganci da tsaro.
Ya ce, aikin ya haɗa da gyaran injina, wayoyin wuta da kuma jikin motocin, lamarin da ya tsawaita rayuwarsu tare da dacewa da ƙa’idojin aiki na zamani.
Injiniya Kofar Soro ya ƙara da cewa an sauya babbar motar Mercedes-Benz 911 zuwa motar aiki “tafi da gidanka”, domin biyan buƙatar ayyukan gwamnati a sassa daban-daban.
Ya jaddada cewa wannan ci gaba na ƙara nuna muhimmiyar rawar da sashen Central Mechanical Workshop ke takawa wajen tallafa wa ayyukan gwamnati ta hanyar amfani da ƙwarewar fasaha da ake da ita a cikin gida.
A cewarsa, hakan zai rage dogaro da kamfanonin waje tare da tabbatar da amfani da dukiyar jama’a yadda ya kamata.
Matasa masu karɓar horo a cibiyar ne suka gudanar da ayyukan gyaran motocin, matakin da ke ba su dama su samu gogewa ta zahiri tare da ƙara kwarewa a sana’ar da suke koya.
