Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dokokin Jiha ta Akwa Ibom na shirin amincewa da wani sabon ƙudirin doka da yake neman haramta duk wata hulɗa ta jima’i tsakanin mata da maza masu aure a cikin jihar.
Wani lauya mai suna Obiavel Albert Abigo ne ya bayyana haka a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, inda ya ce ƙudirin, wanda Mataimakin Gwamna, Sanata Akon Inyang ya ɗauki nauyin gabatarwa, ya tanadi hukunci mai tsauri ga duk wata yarinya, mace ko budurwa da aka samu da laifin yin lalata da namiji mai aure.
A cewarsa, ƙudirin ya bayyana cewa duk macen da aka tabbatar da laifinta za a yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari, ba tare da zabin biyan tara ba. Sai dai namijin da aka samu da laifin zai biya tarar naira miliyan biyu.
Abigo ya ce, ana sa ran majalisar za ta kaɗa ƙuri’a kan ƙudirin a zaman majalisa na ranar Talata, kuma idan aka amince da shi zai zama ɗaya daga cikin dokoki mafi tsauri da aka taɓa gabatarwa kan batun zina a Nijeriya.
Idan ƙudirin ya zama doka, zai kasance karo na farko da wata jiha a Nijeriya ta kafa doka kai tsaye kan zina, duk da cewa a halin yanzu karuwanci ya riga ya kasance laifi a ƙarƙashin dokokin ƙasa.
A wani lamari mai nasaba da haka, Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wata ƙungiyar farar hula ta shigar domin kare karuwai daga tsarewa da cin zarafi a Babban Birnin Tarayya. A hukuncin da Mai shari’a James Omotosho ya yanke a watan Maris 2025, kotun ta ce karuwanci ba shi da kariya a ƙarƙashin doka a Nijeriya.
Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa karuwai na iya fuskantar kamawa da gurfanarwa a ƙarƙashin Kundin Doka na Penal Code, kuma ba su da wani haƙƙi na doka da zai ba su damar gudanar da sana’ar karuwanci a Abuja. Ya ce ƙarar da aka shigar ba ta da tushe kuma ba ta dace da dokokin kare haƙƙin ɗan Adam ba.
ƙungiyar Lawyers Alert Initiative for Protection of Rights of Children, Women, and the Indigent ce ta shigar da ƙarar a kan Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB), Ministan Babban Birnin Tarayya, da kuma Babban Lauyan Tarayya, tana neman kotu ta hana jami’an tsaro kama mata da ake zargi da karuwanci.
Sai dai kotu ta yi watsi da buƙatar, tana mai cewa dokokin Nijeriya sun riga sun haramta karuwanci, kuma jami’an tsaro na da ikon kama duk wanda ake zargi da aikata laifin. Mai shari’a Omotosho ya ƙara da cewa haƙƙoƙin ɗan Adam ba su da cikakkiyar ’yanci, domin ana iya taƙaita su idan hakan zai kare tsari, ɗa’a da tsaron al’umma.
