Cece-kuce ya ɓarke yayin da Olubadan ya ƙi amsa gaisuwar Alaafin

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An samu cece-kuce a Ibadan bayan da Olubadan na ƙasar Ibadan, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, ya yi watsi da gaisuwar Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade, a wani taron addinai da aka gudanar a babban birnin jihar Oyo.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a yayin wani taron haɗin kan addinai da gwamnati ta shirya a filin taro na sakatariyar gwamnati da ke bayan Majalisar Dokokin Jihar Oyo a Agodi, Ibadan.

A wani faifan bidiyo da shafin Oyo Affairs ya wallafa, an ga Alaafin yana zaune yana miƙa hannu domin gaisawa da Olubadan da ya iso wurin taron. Sai dai Olubadan bai amsa gaisuwar ba, inda ya ci gaba da tafiya bayan ya gaishe da Gwamna Seyi Makinde da wasu manyan baƙi, ya nufi kujerarsa kai tsaye ba tare da kulawa da hannun Alaafin da ya miƙo ba.

Wannan al’amari ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta da kuma tsakanin masu lura da harkokin gargajiya, inda ake ta muhawara kan dokokin ladabi, martabar sarakuna da kuma mutunta juna a tsakanin sarakunan Yarbawa. 

Wasu sun bayyana lamarin a matsayin wata alama ta rikici da ke ta kunno kai a cikin tsarin gargajiya na jihar Oyo, yayin da wasu ke kira da a yi hattara wajen fassara abin da ya faru, tare da jaddada muhimmancin girmama al’adu da dokoki na gargajiya.

Taron na haɗin kan addinai, wanda ya samu halartar shugabannin addinai, jami’an gwamnati da sarakuna, an shirya shi ne domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mabiya addinai daban-daban a jihar. Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa ta hukuma daga fadar Olubadan ko ta Alaafin dangane da abin da ya faru.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan batun fifiko da rawar da sarakuna ke takawa a Majalisar Sarakunan Jihar Oyo, duk da cewa sarakunan biyu sun taɓa halartar taruka tare a baya, ciki har da wani taron sirri da suka yi da Gwamna Makinde a ƙarshen shekarar 2025.

By ukarofi