Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima za su kashe jimillar kuɗi har Naira biliyan 9.36 a shekarar 2026 wajen tafiye-tafiye na cikin gida da na waje, tare da kuɗin ciyarwa da hidimar abinci, kamar yadda ke ƙunshe a cikin daftarin kasafin kuɗin shekarar da gwamnati ta gabatar.
Wannan bayanai na cikin takardun kasafi da Ofishin Kasafin Kuɗin Tarayya ya fitar, bayan da Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 58.18 a gaban Majalisar Dokoki a ranar 19 ga Disamba, 2025.
A jawabinsa lokacin gabatar da kasafin, Shugaban ƙasa ya bayyana cewa tsaron ƙasa zai ci gaba da kasancewa ginshiƙin bunƙasuwar tattalin arziki, janyo jarin waje da kuma tabbatar da zaman lafiya, abin da ya bayyana a yadda aka ware manyan kuɗaɗe ga muhimman sassa.
Bayanai dalla-dalla a daftarin kasafin mai shafuka 2,790 ya nuna cewa Shugaba Tinubu shi kaɗai an kiyasta zai kashe Naira biliyan 7.01 wajen tafiye-tafiye na cikin gida da na ƙasashen waje a shekarar 2026. Haka kuma, an ware masa Naira miliyan 431.62 domin sayen kayan abinci, kayan girki, shan shayi da sauran hidimomin ciyarwa.
A bangaren Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, takardun sun nuna cewa zai kashe Naira biliyan 1.73 wajen tafiye-tafiye, sai kuma Naira miliyan 186.03 da aka ware domin ciyarwa da hidimar abinci.
An nuna cewa a kasafin tafiyar Shugaban ƙasa, Naira miliyan 873.89 an ware su domin tafiye-tafiye na cikin gida, yayin da Naira biliyan 6.14 aka ware domin tafiye-tafiye na waje. A ɓangaren Mataimakin Shugaban ƙasa kuwa, Naira miliyan 417.49 an tanada su domin tafiyar cikin gida, sai Naira biliyan 1.31 na tafiyar ƙasashen waje.
Baya ga tafiya da ciyarwa, kasafin ya nuna cewa Shugaba Tinubu zai kashe Naira miliyan 65.77 wajen ladan zama a taro da wasu alawus-alawus. Haka kuma, an ware Naira miliyan 895 domin sayen littattafan ɗakin karatu da kayan aiki a fadar shugaban ƙasa.
A ɓangaren ayyukan raya ƙasa, kasafin ya tanadi Naira miliyan 179 domin sayen motocin aiki, Naira miliyan 778.6 domin kayan ofis da kayan ɗaki, sai Naira miliyan 1.34 domin kayan lafiya da na jinya.
Takardun sun kuma nuna cewa Naira miliyan 89.5 an ware su domin ci gaba da sayen motocin alfarma na SUV ga Shugaban ƙasa da Mataimakinsa.
A matakin ƙasa gaba ɗaya, kasafin shekarar 2026 ya ware Naira tiriliyan 3.2 ga ɓangaren tsaro, Naira tiriliyan 2.3 ga ilimi, Naira tiriliyan 2.1 ga lafiya da walwalar jama’a, Naira tiriliyan 1.4 ga noma da tsaron abinci, sai Naira tiriliyan 1.0 ga Hukumar Zaɓe ta ƙasa INEC.
