Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rikici ya ɓarke a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) ranar Litinin, bayan wasu ’yan kasuwa daga Kano sun yi zanga-zanga a ofishin kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines, suna zargin ma’aikatan kamfanin da lalata jakunkunan fasinjoji da kuma satar kayayyaki masu daraja.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan kasuwar, da yawansu ke sana’ar sayar da na’urorin lantarki da kayayyakin shigo da su daga ƙasashen waje, sun koka da abin da suka kira sakaci da maimaituwar satar kaya daga jakunkunan fasinjoji, musamman a jiragen da ke bi ta Addis Ababa.
Zanga-zangar ta biyo bayan isowar wasu fasinjoji daga Saudiyya ta Addis Ababa a ranar Lahadi.
A cewar masu zanga-zangar, an karkatar da jirginsu zuwa Abuja kafin daga bisani ya sauka a Kano ba tare da jakunkunansu ba.
Sun ce an kawo jakunkunan washegari, amma da suka buɗe, sai suka tarar an yayyaga wasu akwatuna tare da batan kayayyaki masu muhimmanci.
ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Bashir Ali, ya ce ya daɗe yana fuskantar irin wannan matsala a duk lokacin da ya yi amfani da jiragen Ethiopian Airlines.
Ya bayyana cewa, sau da dama yana tilasta masa mayar wa kwastomominsa kuɗi sakamakon satar kayayyaki daga jakunkunansa.
“Wannan abu ya daɗe yana faruwa,” inji Ali, “sau da dama na riga na mayar wa kwastomomi kuɗinsu saboda kayansu sun ɓace. Gaskiya ya isa haka.”
Wani ɗan kasuwa mai sayar da wayoyin salula a Kano, Haruna Wada, ya ce an yayyaga jakunkunansa tare da satar wayoyin iPhone 17 masu daraja miliyoyin Naira. Ya ce, idan ba a biya shi diyyar asarar kayansa ba, zai garzaya kotu domin neman haƙƙi. “Idan wannan kamfani bai biya ni kuɗin kayana ba, lauyoyina a shirye suke. Za mu nemi adalci a kotu. Ya isa haka,” inji shi.
Ita ma Waleeda Abdallah ta ce wannan matsala ta zama ruwan dare ga masu amfani da kamfanin, lamarin da ke bata sunan Ethiopian Airlines a idon jama’a.
Ta ce fasinjoji sun daɗe suna kuka kan batan kaya da satar jakunkuna, amma hukumomi ba su ɗauki tsauraran matakai ba.
=A yayin zanga-zangar, shugabar ofishin Ethiopian Airlines a Kano ta yi jawabi ga masu zanga-zangar, inda ta roƙe su da su kwantar da hankali, tana mai cewa ana gudanar da bincike kan zarge-zargen. Ta yi alƙawarin cewa kamfanin zai ɗauki matakan da za su hana faruwar irin haka nan gaba, kodayake ba a bayyana batun biyan diyya a take ba.
A wani ɓangare kuma, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta tabbatar da cewa Ethiopian Airlines ta biya dukkan tarar da aka ƙaƙaba mata a baya kan take haƙƙoƙin fasinjoji. Daraktan hulɗa da jama’a na NCAA, Michael Achimugu, ya bayyana hakan a shafinsa na ɗ, inda ya ce a watan Disambar 2024 an hukunta wasu kamfanonin jiragen sama guda biyar bisa karya dokokin kare haƙƙin fasinjoji.
Ya ce, laifuffukan sun haɗa da jinkirta mayar da kuɗi, rashin amsa umarnin NCAA, batan kaya, lalata jakunkuna, jinkirin jirage da soke su. A cewar hukumar, dukkan kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje da aka hukunta, ciki har da Ethiopian Airlines, sun biya tarar da aka ƙaƙaba musu.
Hukumar ta jaddada cewa waɗannan matakai ba don hukunci ba ne, sai dai domin inganta ayyukan kamfanonin jiragen sama da kuma kare haƙƙin fasinjojin da ke amfani da su a Nijeriya.
