Hukumar Haraji ta Sakkwato ta dakatar da tsarin shigar da bayanan haraji kowane wata

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Haraji ta Jihar Sakkwato (SOIRS) ta janye umarnin da ta bayar na tilasta masu biyan haraji su riƙa shigar da bayanansu ta hanyar intanet kowane wata, inda ta bayyana cewa a halin yanzu ana buƙatar ne kawai a shigar da bayanan haraji na shekara-shekara ta yanar gizo.

Hukumar ta fitar da wannan bayani ne a wata sanarwa da ta wallafa a ranar Alhamis, biyo bayan martanin jama’a kan wata takarda da ta fitar a ranar 5 ga Janairu, wadda ta bayyana fara aiwatar da tsarin shigar da bayanan haraji kowane wata ta intanet.

A cewar SOIRS, an dakatar da wannan umarni ne saboda rashin kammala tsarin da ake buƙata domin aiwatar da shigar da bayanan haraji kowane wata ta yanar gizo.

Hukumar ta ce tsarin aiwatar da shirin bai kammala ba har yanzu, kuma ba a fara amfani da shi gaba ɗaya ba.

Hukumar ta shawarci masu biyan haraji da su yi watsi da duk wani bayani da ke nuna cewa wajibi ne a shigar da bayanan haraji kowane wata ta intanet har sai an sake sanarwa.

Sai dai ta jaddada cewa shigar da bayanan haraji na shekara-shekara ta yanar gizo na nan daram kamar yadda Dokar Kula da Haraji ta Nijeriya ta shekarar 2025 ta tanada.

SOIRS ta bayyana cewa tsarin shigar da bayanan haraji ta intanet na daga cikin manyan gyare-gyaren da take aiwatarwa, inda ta ce wannan tsari na taimakawa wajen ƙara inganci, gaskiya da sauƙaƙa bin doka ga masu biyan haraji.

Hukumar ta ce, za ta ci gaba da hulɗa da masu biyan haraji, tare da ba su shawarwari da goyon baya domin sauƙaƙa musu bin sabbin tsare-tsaren da ake aiwatarwa a hankali.

A ƙarshe, SOIRS ta tabbatar da cewa tana nan daram wajen inganta tsarin haraji da ayyukan da ta ke bai wa jama’a a faɗin jihar.

By ukarofi