
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma a Legas sun shiga halin cece-kuce bayan rasuwar wasu ‘yan biyu masu kimamin watanni tara da haihuwa a ƙasa da sa’o’i 24 da yi musu allurar rigakafi a wani asibitin gwamnati (PHC) da ke Ƙaramar Hukumar Ojo a jihar.
An ruwaito cewa, yaran masu sunaye Testimony da Timothy, an kai su Ajangbadi Primary Health Centre ne a safiyar ranar 24 ga watan Disamba, 2025 a inda suka rasu a washegari, wato safiyar Kirsimeti, lamarin da ya haddasa cece-kucen musamman akan neman a yi bincike tare da tabbatar da adalci akan waɗanda abin ya shafa.
Mahaifinsu mai suna Samuel Alozie da aka fi sani da Promise Samuel a kafafen Soshiyal Mediya, ya yi zargin cewa ‘ya’yan nasa jim-kaɗan bayan rigakafin sun fuskanci matsanancin rashin kuzari, wanda daga nan ba su sake samun sauƙi ba.
A cewarsa, yaran lafiyarsu ƙalau gabanin a yi musu rigakafin. Ya ce ba da jimawa ba da yin allurar sai suka shiga halin rashin kuzarin.
Akan haka ne wata malamar asibiti ta shawarce shi da ya ba su maganin paracetamol matuƙar suka cigaba da kasancewa cikin halin, inda a cewarsa, ya bi umarnin nata saidai duk da haka ba a samu sauyi ba.
Bayan rasuwarsu ne Mista Promise Samuel ya zargi asibitin da sakaci da cewa ta yiwu allurorin da aka yi musu waɗanda kwanaki aikinsu suka ƙare ne, baragurbi, sama da kima ko rashin amfani da su ta yadda ya dace.
Ya kuma yi ikirarin an bai wa yaran maganin tsutsar ciki ba tare da sanar da shi ba, inda ya ƙara da cewa bai ma san wanda ya yi wa yaran rigakafin ba.
Kazalika, ya ƙaryata ikirarin jami’an asibitin cewa yaran sun rasu ne a sanadiyyar cin abincin da wata ƙwayar cuta ke ciki, yana mai kira ga lauyoyi, ƙungiyoyi masu zaman kansu da ɗaukacin al’umma da su kai masa ɗauki akan al’amarin.
