Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Kungiyar Wayar da Kan Jama’a ta Birni da ƙauye a Jihar Zamfara ta bayyana goyon bayanta ga ɗan majalisar tarayya Hon. Abdulmalik Zubairu (Zannan Bunguɗu) wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Maru/Bungudu a jihar Zamfara domin cika burinsa na siyasa a shekarar 2027.
ƙungiyar ta bayyana jarumtarsa da shugabanci da kuma wakilci nagari a matsayin manyan dalilan da suka sa suka amince da su goyi bayansa.
ƙungiyar ta miƙa wa ɗan majalisar tarayyar man shafawa kimanin 2,000 na Pomades (ɓaciline) a matsayin wani ɓangare na goyon bayansu ga harkokin siyasarsa.
Sun bayyana cewa hakan na nuni da tabbatar da nasarar ɗan majalisar tarayya a duk wani yunƙurinsa na siyasa zuwa ga babban zaɓen 2027.
A cewar ƙungiyar, farfaɗo da tattalin arziki da sauran ayyukan jinƙai da aka yi a faɗin jihar Zamfara ta hannun Hon. Zanna ba wai kawai a mazaɓarsa ba har ma a faɗin jihar abinda a yana ne.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Gusau, mai shirya taron kuma Shugaban ƙungiyar Wayar da Kan Jama’a ta Birni da Kauye, Alhaji Isyaka Lawali Gusau, ya ce ƙungiyar ta gamsu cewa Abdulmalik Zannan Bungudu shine mutumin da ya dace ya zama shugaba a Jihar ta Zamfara.
“Ba muna goyon bayansa ne don amfanin kashin kai ba, sai don tabbatar da ci gaba da nasarar shugabancinsa na siyasa,” ya ce.
Ya yaba wa Hon. Abdul Malik kan sake gina asibitoci, gyaran masallatai daban-daban, da kuma aurar da marayu 150 a mazaɓarsa a matsayin babban cigaba da ɗan Majalisa Zanna ya yi a Jihar ta Zamfara.
Ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta cigaba da bayar da dukkan goyon bayansu ga Hon. Abdul Malik Zubairu don cimma burinsa na siyasa a shekarar 2027 a jihar Zamfara.
