Alƙalin Gombe ya kira a koma kan kyawawan ƙa’idoji don daƙile kashe-kashe a Nijeriya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Wani alƙalin kotun Lardi (Upper Area Court) a Jihar Gombe kuma Shugaban ƙungiyar alkalan kotunan lardi na jihar, Mai Shari’a Abubakar Usman Malala, ya yi gargaɗin cewa yawaitar kashe-kashe da ta’addanci a Najeriya ba za su ragu ba sai al’umma sun koma kan muhimman ƙa’idojin tarbiyya da addini.

Mai Shari’a Malala ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilinmu, yayin da yake tsokaci kan kisan wata mata da ’ya’yanta shida a Jihar Kano, lamarin da ya girgiza ƙasar baki ɗaya.

Ya ce ƙaruwar tashin hankali alama ce ta rushewar kyawawan ɗabi’u da a da ke kare rayuka da zaman lafiya a cikin al’umma.

Ya ƙara da cewa manyan malamai na addini, ciki har da Abu Ishak a littafinsa Al-Muwafaqat, sun fayyace tubalan zaman lafiya da kare mutunci da rayuwar ɗan Adam.

A cewarsa, ginshiƙi na farko shi ne bin addini na gaskiya, inda ya jaddada cewa koyarwar addini tana hana zalunci, cutarwa da zubar da jinin wanda bai ji ba bai gani ba.

Na biyu kuwa shi ne kare dukiya, yana mai cewa idan mutane suka mutunta abin da ya shafi na wani, za a rage sata, rikici da ɗaukar fansa.

Mai Shari’a Malala ya bayyana na uku da cewa kare rayuwa, yana nuna cewa addini da doka sun tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda ya kashe wani ba tare da haƙƙi ba, domin tsoratar da masu shirin aikata laifi.

Na huɗu shi ne kare hankali, wato hana shaye-shaye da miyagun ƙwayoyi da ke gusar da tunani, inda ya ce yawancin laifuka ana aikata su ne sakamakon maye da shan ƙwayoyi.

Na biyar kuma shi ne kare asali da mutuncin ɗan Adam, wanda ya haɗa da hana zina, fyaɗe da duk wani aiki da ke rushe martabar mutane da zaman lafiyar iyali.

Alƙalin ya kuma nuna damuwa kan yawaitar kashe-kashe a ƙasar, yana cewa masu laifi kan ƙara samun ƙarfin guiwa idan shari’a ta yi jinkiri ko aka nuna wariya.

Ya buƙaci hukumomin tsaro da su garzaya da gurfanar da masu laifi a kotu, tare da kiran alƙalai da su yi adalci cikin gaggawa ba tare da tsoro ko son zuciya ba.

“Adalci cikin sauri yana rage yawan masu shirin aikata laifi,” in ji shi.

Mai Shari’a Malala ya kuma shawarci iyaye da su ba tarbiyyar ’ya’yansu muhimmanci, yana mai cewa yawancin matsalolin tsaro suna farawa ne daga rashin tarbiyya a gida, ba wai gazawar gwamnati kaɗai ba.

Ya kuma gargaɗi shugabanni da jami’an gwamnati da kada su yi shiru kan abin da bai dace ba saboda tsoron masu iko.

“Shiru kan zalunci yana ƙara ƙarfafa masu laifi tare da lalata tsaro,” in ji shi.

Da yake Allah wadai da kisan da aka yi a Kano, Mai Shari’a Malala ya bayyana aikin a matsayin abin takaici, rashin imani da kuma abin da bai dace da bil’adama ba, yana kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai wajen dawo da tarbiyya, adalci da girmama rayuwar dan Adam.

By ukarofi