Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
“Yarjejeniyar COSMOS ta ₦155bn za ta samar da gidaje a Kankia, Katsina, Daura da Funtua.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana haka bayan da ya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da kamfanin COSMOS Residential City Nigeria Limited.
Gwamnan ya ce kamar yadda yarjejeniyar haɗin gwiwa take za a gina gidaje 3,750 a garuruwan Kankia da Raɗɗa, gidaje 2,500 a Kankia da Raɗɗa kuma guda 1250 ƙarƙashin sabon tsarin agro-residential, wanda darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 155 (₦155bn).
“Wannan yarjejeniya sakamakon tsare-tsare masu kyau ne, bincike mai zurfi da amincewa da juna. Mun ƙuduri aniyar cika dukkan alƙawarin da Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauka domin wannan haɗin gwiwa ya ɗore kuma ya amfani al’ummarmu,” in ji Gwamnan.
Ya bayyana cewa aikin, wanda za a kammala cikin watanni 16 zuwa shekaru biyu, zai haɗa gidaje na zamani da kiwon kifi a bayan gida da kuma lambunan kayan marmari a kowane gida, domin samar da hanyoyin dogaro da kai ga masu cin gajiyar shirin tare da ƙara yawan samar da abinci na cikin gida da na fitarwa zuwa ƙasashen waje.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta riga ta ware filaye don aikin a Kankia da Raɗɗa, kuma za ta tantance matasa marasa aikin yi da iyalai masu ƙaramin ƙarfi, ciki har da waɗanda ba su yi karatun boko ba amma suna da ƙwarewar noma da sana’o’in hannu, a matsayin masu cin gajiyar shirin.
“An tsara wannan shiri ne domin ƙarfafa matasanmu da ƙananan iyalai. Kowane gida da ya ci gajiyar shirin zai samu gida cikakke da kayan ɗaki, horo kan hanyoyin noma na zamani, sa ido kan gona ta hanyar fasahar zamani (digital), da damar kai kayayyakin su zuwa kasuwannin duniya,” in ji Gwamna Raɗɗa.
Ya ƙara da cewa ana sa ran kowane mai cin gajiyar shirin zai rika samun kuɗin shiga har Naira dubu 200 (₦200,000) a kowane wata, tare da tsarin ajiya na dole tsakanin Naira dubu 50 zuwa 70 (₦50,000–₦70,000) domin rage kuɗin jarin masu zuba jari.
Dikko ya ce bayan haka, gidaje da gonakin za su zama mallakin masu cin gajiyar shirin cikin shekaru uku zuwa biyar.
Gwamnan ya bayyana cewa tuni aka miƙa filin aikin ga kamfanin, yayin da COSMOS ta yi alƙawarin fara aikin nan da kwanaki 10 ta hanyar cika shiri gaba ɗaya a wurin.
A jawabinsa a wajen taron ,shugaban ma’aikata na Jihar, Alhaji Falalu Bawale, ya ce aikin zai samar da gidajen noma 3,750 tare da mai da hankali sosai kan ƙarfafa matasa, koyon sana’o’i, wadatar abinci da ci gaban al’umma.
Haka kuma, manajan darakta na COSMOS Residential City Nigeria Limited, Murtala Sani Ibrahim, ya ce ana aiwatar da aikin ne tare da haɗin gwiwar kamfanin SuperEye USA Corporation da ke ƙasar Amurka,kuma ya tabbatar da cewa ’yan kwangila, masu sana’a da masu samar da kayayyaki na cikin gida a Kankia da Raɗɗa za su samu fifiko.
Ya ƙara da cewa daga baya za a faɗaɗa shirin zuwa Katsina, Daura da Funtua a mataki na biyu, tare da kiran dukkan masu ruwa da tsaki da su ba da goyon baya da haɗin kai domin nasarar aiwatar da shirin.
Aikin gidajen kashi na farko za a fara a garin Kankia a ƙaramar hukumar Kankia da garin Raɗɗa a karamar hukumar Charanchi.
Sai kashi na biyu da zai haɗa da Katsina, Daura da Funtua.
