Mutanen Daura ba su yanke hukuncin takarar Tinubu da Dikko ba a zaɓen 2027, inji Nalado

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai magana da yawun yan kishin Daura Hon Lawal Nuhu Nalado ya faɗi haka a wani taron manema labarai da ya gudana a garin Daura.

Nalado wanda tsohon shugaban jam’iyar Accord party na ƙasa ya ce maganan da manyan ya’yan jam’iyar APC su kayi cewa al’ummar ƙaramar hukumar Daura sun amince da takardar Tinubu da Dikko Raɗɗa a zaɓen 2027 ba gaskiya bane”sun ari bakin yan Daura ne suka ci masu albasa,”Inji shi.

Ya bayyana takaicin sa yadda su jigajigan jam’iyar APC suka kira taron da bai wuce mutane 50 har suka zartar da wannan matsaya ba tare da sanin masu ruwa da tsaki ba na yankin ba.

Nalado wanda harwala yau tsohon shugaban gamayyar jam’iyyun siyasa na ƙasa ya ce ba su yarda da wannan mataki “kamar yadda kuka gani wannan taron ya haɗa da ya’yan jam’iyun ne na APC, PDP,APGA,ADC da sauran su,a da suma suka koka kan wannan yanke hukunci da yan APC su kayi domin buƙatar kan su,”ya ce.

Ya ce su ba sa dawo da APC sai adawa da ya’yan jam’iyar da suka gudanar da wannan taron” kuma mazan mu da matan mu muna kira ga waɗannan mutane da suyi gaggawar janye waɗannan kalamai da sukayi da kayan sunyi ne da yawun al’ummar Daura.

Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina da shugaban jam’iyar APC ta jihar da wasu manyan jam’iyar suka shirya taro a sakatariyar ƙaramar hukumar Daura inda suka jaddada goyon bayan al’umma Daura kan zaɓen Tinubu da Dikko Raɗɗa a 2027.

Ɗimbin matasa da mata suka halarci taron yan kishin ƙasa na ƙaramar hukumar Daura.

By ukarofi