Kotu ta ba Yahaya Bello damar tafiya Umara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta amince wa tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da buƙatarsa ta neman tafiya Saudiyya domin gudanar da aikin Umara a ƙasa mai tsarki.

A lokacin da yake gabatar da hukunci yayin zaman, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya umarci a sake fasfo ɗin Yahaya Bello da da kotun ta bayar da uamrnin a ƙwace shi na wucin-gadi.

Ana gudanar da shari’ar Bello ne bisa tuhume-tuhumen da suka shafi sauya akalar wasu maƙudan kuɗaɗe da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta maka shi akansu.

A ranar 20 ga watan Junairu aka rubuta takardar neman izinin tafiyar tare da ta ‘affidavit’ mai sakin layi 24 daga ɓangaren Yahaya Bello, wadda lauyansa, Mista Joseph Daudu (SAN) ya jagoranci gabatarwa.

Lauyan ya sanar da kotun cewa sun nemi haka ne da nufin ba Yahaya Bello damar yin Umara a watan Ramadana kasancewar ya shafe sama shekaru takwas bai je ƙasa mai tsarki ba.

Saboda haka ne yake neman a ba shi damar tafiya ƙasar domin neman Allah ya ba shi nasara akan shari’ar da EFCCn ta maka shi a kai.

A ɓangaren EFCC, Lauya Kemi Pinheiro (SAN) ya ce ba za su ja da buƙatar tafiyar wanda ake tuhuma ba, saidai ba za su amince da soke wata rana da daga cikin ranakun da kotun ta ware domin cigaba da shari’ar ba.

Baya ga haka ne alƙalin ya amince da buƙatar tare da umartar da sake wa tsohon gwamnan fasfo ɗin nasa don samun damar tafiyar.

By Babaji