A cikin wani rahoton da ƙungiyar Majalisar ɗinkin Duniya ta fitar a ranar Talata, an bayyana cewa fiye da 37,000 Falasɗinawa ne aka tilasta su barin gidajensu a shekarar 2025 a Yammacin Banki (West Bank), yawanci dalilin irin aayyukan ɓarna da sojojin Isra’ila ke aikatawa da sunan matakan tsaro waɗanda suka shafi sansanonin ‘yan gudun hijira. Wannan adadi ya jawo ƙarin damuwa daga ƙasashen duniya, waɗanda ke kira ga ɗaukar matakin rage tashin hankali da tallafa wa waɗanda rikicin ya shafa.
Rahoton ya ce wannan ƙaura ta tilastawa ta faru ne a lokacin da ake ƙoƙarin sake ƙoƙarin kwaɗaita zaman lafiya da kuma rage hare‑haren da ke shafar farar hula. Hukumar UN ta jaddada cewa rasa rayukan mutane da durƙushewar tattalin arzikin na ƙara wa matsalar muni, da kira ga ƙasashen duniya da su ci gaba da tura kayan agaji da tallafi ga waɗanda aka tilasta barin gidajensu.
