Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin horar da ’yan Nijeriya miliyan 10 akan hada-hadar kuɗi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya Nijeriya ta ƙaddamar da shirin horar da ’yan ƙasa guda miliyan 10 kyauta akan ilimin hada-hadar kuɗi da shigar kuɗi bisa tsari, inda ta ce matasa da mata ne ginshiƙin cin gajiyar yawan al’ummar ƙasar.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja da yake wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron.

Ya ce, ba za a iya gina tattalin arziƙin dala tiriliyan daya ba tare da kwararrun ma’aikata, nagartattun ka’idoji da ingantaccen tsarin sana’o’i ba.

A yayin taron, Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ta hannun Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Hada-hadar Kudi da Tattalin Arziki (PreCEFI) ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da manyan kungiyoyin kwararru shida da suka hada da ICAN, CIBN, CIS, NICA, CRMI da NIIE.

Yarjejeniyar na da nufin tsara horo, bada takardar shaidar kwarewa, amfani da fasahar zamani da tsarin tallafi domin karfafa gwiwar ’yan kasuwa, musamman mata da matasa.

Shettima ya ce hada-hadar kuɗi ba ta tsaya ga samun dama kaɗai ba, sai an samu ilimi, ƙwarewa da amana domin tabbatar da sarrafa su akan tsari.

Shugaban ICAN, Mallam Haruna Nma Yahaya, ya yabawa gwamnatin Tinubu bisa gyare-gyaren tattalin arziki da suka haifar da kaddamar da shirin. Ya tabbatar da cikakken goyon bayan kungiyoyin kwararru wajen ganin an cimma nasarar shirin.

Haka nan, Shugaban WAWU Africa, Emmanuel Lennox, ya ce sun shirya samar da dandamalin zamani da kayan aiki da za su tabbatar da ingancin horon.

Kazalika, an bayyana cewa shirin na da muhimmanci domin rage ficewar jama’a daga tsarin hada-hadar kuɗi sakamakon ƙarancin ilimi da ƙwarewa.

By Babaji