Ƙungiyoyin ƙwadago za su yi gangamin goyon bayan ma’aikatan Abuja a yau

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (NLC) da Ƙungiyar Kasuwanci (TUC) sun ce za su gudanar da gangamin lumana a yau Talata, 3 ga watan Fabarairu, domin nuna goyon baya ga kwamitin haɗaka na ƙungiyoyin ma’aikata (JUAC).

Ƙungiyoyin sun sanar da haka ne a Abuja ta wata takardar haɗaka mai ɗauke da sanya hannayen Babban Sakataren NLC, Benson Upah da Nuhu Toro, wanda shi ne na Babban Sakataren TUC.

Za su gudanar da tattakin ne da nufin nuna goyon bayansu ga yajin aikin ma’aikatan Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCDA) ƙarƙashin jagorancin JUAC bisa albashin da ba a biya su ba.

A ranar 19 ga watan Junairu ma’aikatan da ke ƙarƙashin JUAC suka tsunduma yajin aikin, wanda ya sa suka kulle wasu muhimman ofisoshi ciki har da sakatariyar FCTA da FCDA.

Hakan ya biyo bayan ƙarewar wa’adin 7 ga Junairu da suka ba wa hukumar gudanarwar FCTA na ta warware matsalolinsu da aka jima ana ƙoƙarin shawo kansu waɗanda suka shafi haƙƙoƙi da walwalar ayyukansu.

A cewar ƙungiyoyin ƙwadagon, sun ɗauki matakin ne don nuna damuwarsu akan matsin da aka sanya takwarorinsu aciki, wanda zai taimaka wajen magance matsalolin takura da rashin adalci ga ma’aikata.

Sun ƙara da cewa, goyon bayan nasu za ta cigaba da kasancewa cikakkiya ga mambobin JUAC, suna masu kira ga jagororinsu na jihohi da su bada haɗin kai wajen gudanar da gangamin.

By Babaji