Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban masu ruwa da tsaki a jam’iyar APC a jihar Katsina Alhaji Salisu Mamman kaɗanɗanni ya miƙa buƙatar haka ga dimbin magoyan ya’yan da suka taru a filin wasa na Muhammadu Dikko a Katsina.
A yayin taron, Manyan jiga-jigai da shugabannin Jam’iyar a Jihar Katsina sun bayyana cikakkiyar amincewarsu ga shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, , da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, a matsayin ‘yan takarar Shugaban ƙasa da Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
A jawabinsa bayan amince da buƙatar,shugaban masu ruwa da tsaki na APC a jihar Katsina, Alhaji Salisu Mamman Kadandani, ya bayyana cewa wannan amincewa ta biyo bayan tattaunawa mai faɗi da kuma kawo buƙatar tarar a gaban magoya bayan jam’iyar da aka yi a faɗin jihar, tare da kimanta nasarorin shugabanci da ayyukan gwamnati a matakin ƙasa da jiha.
Ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziƙi, matakan tsaro, gina manyan ababen more rayuwa, da aiwatar da manufar Renewed Hope na Shugaba Tinubu na ɗora Najeriya kan tafarkin ci gaba mai ɗorewa. Haka kuma ya jaddada cewa gwamnatin Gwamna Raɗɗa ta nuna gaskiya, tsari, da inganta rayuwar al’ummar Jihar Katsina, inda ya ce ci gaba da wannan shugabanci bayan 2027 na da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa.
A nasa jawabin karɓar amincewar, Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya nuna godiyarsa ga shugabannin jam’iyya da jiga-jiga bisa irin amincewa da aka nuna masa yana mai bayyana hakan a matsayin ƙarin nauyi da alhaki na ci gaba da yi wa al’umma hidima cikin gaskiya da riƙon amana. Ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da mayar da hankali kan tsaron rayuka da dukiyoyi, bunƙasa noma, inganta ilimi, kiwon lafiya, da shirye-shiryen tallafa wa al’umma tare da kara haɗin gwiwa da Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu domin aiwatar da shirye-shiryen da za su shafi rayuwar alumma kai tsaye.
Haka nan, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe, ya karɓi wannan amincewa a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya yaba wa Jihar Katsina bisa haɗin kai da nuna balagar siyasa.
Ya bayyana amincewar a matsayin shaida ta yarda da jagoranci da sauye-sauyen da shugaban ƙasa ke aiwatarwa, tare da kira ga mambobin jam’iyya da su ci gaba da haɗin kai, su guji rarrabuwar kai, kuma su ƙara jajircewa don tabbatar da nasarar jam’iyyar a shekarar 2027.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sen. Barau I. Jibrin, ya yabawa irin haɗin kan da aka nuna a tsakanin ‘ya’yan APC a Katsina, yana mai bayyana wannan mataki a matsayin wanda ya dace da lokaci. Ya yaba da shugabancin Shugaba Tinubu a daidai wannan lokaci a tarihin ƙasa tare da yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa salon mulkinsa wanda ya mayar da hankali kan jin walwalar jama’a, inda ya yi kira ga ‘yan jam’iyya da suyi amfani da wannan haɗin kai don samar da cigaba ga jihar.
Shima a nasa jawabin, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Alhaji Aliyu JB Daura, ya tabbatar da cewa jam’iyyar a jihar a shirye take tsaf domin tunkarar zaɓen 2027, yana mai cewa wannan amincewa ta nuna ra’ayi ɗaya na mambobin jam’iyya a faɗin jihar. Ya tabbatar wa shugabancin ƙasa cewa za a ƙara himma wajen haɗa kan ‘ya’yan jam’iyya, sasanta rikice-rikice domin samun gagarumar nasara ga APC a dukkan matakai.
Haka zalika, a wajen taron an karɓi dubban mutane daga jam’iyyun adawa a faɗin jihar Katsina da suka dawo jam’iyyar APC tare da nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa da kuma gwamnan jihar Katsina da jam’iyyar a kowane mataki.
Bayan nan an ƙaddamar da rabon motoci ga shugabannin shirin Renewed Hope Ambassadors guda 34 wanda aka ƙaddamar jiya.
Taron ya samu halartar manyan shugabanni da jiga-jigan jam’iyya daga sassa daban-daban na ƙasa.
Daga cikin waɗanda suka halarta akwai shugaban jam’iyyar APC na ƙasa tare da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), Ministar al’adu, Barr Hannatu Musawa, mataimakin Shugaban majalisar dattawa, mataimakan gwamnonin jihohin Yobe da Jigawa, zaɓaɓɓun sanatoci, yan majalisu, ciyamomi, kansiloli, manyan jami’an gwamnatin Jihar Katsina, shugabannin jam’iyya, zaɓaɓɓun wakilai, shugabannin gargajiya, shugabannin mata da matasa.
