
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin masu ibada 80 da wasu ‘yan bindiga suka yi awon-gaba da su a Cocin Ƙaramar Hukumar Kajurum Jihar Kaduna suka koma cikin iyalansu.
Mai garin Kurmin Wali, Ishaku Ɗan’azumi ne ya sanar da haka ga manema labarai a jiya Lahadi, inda ya ce wasu daga cikin mutanen su 166 da aka sacen, sun yi nasarar tserewa daga komar ‘yan bindigar.
A cewarsa, rahotanni da fari sun ce mutane 177 ne aka yi garkuwa da su, amma daga bisani an gano cewa 80 daga cikinsu sun tsare, waɗanda suka samu mafaka a wasu ƙauyuka.
Ya kuma ce har yanzu 86 daga ciki suna cigaba da zama a komar ‘yan bindigar, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da ke cigaba da kasancewa ƙunci a zukatan iyalansu.
Mai garin ya kuma yi magiya ga gwamnati da hukumomin tsaro da su yi hoɓɓasa wajen ganin an ceto sauran waɗanda ke hannun sauran mutanen.
Tuni dai Kakakin Rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan ya ce za su fitar da cikakken bayanai akan al’amarin mutanen Kurmin Wali da aka sace.
