
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya jaddada ƙudirin hukumar na yin cikakken shiri akan lokaci da tsari domin tabbatar da gudanar da Hajjin 2026 ba tare da tangarda ba.
Farfesa Usman ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, inda ya ce NAHCON na tafiya da manufofin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, musamman manufar Ajandar Sabunta Fata da ke mayar da hankali akan walwala da jin daɗin maniyyata a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa hukumar na aiki ne ƙarƙashin kulawar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, tare da ba da fifiko ga kammala muhimman shirye-shiryen aikin Hajji cikin lokaci, musamman batun masaukin maniyyata a birnin Makka, bisa ƙa’idojin hukumomin Saudiyya.
Akan wannan tsari ne Farfesan ya amince da tura tawagar manyan jami’ai zuwa Ƙasar Saudiyya domin kammala da kuma karɓar duk wasu shirye-shiryen masauki da ke saura a Makka, don kauce wa duk wata matsala ta jinkiri.
Tawagar za ta ƙunshi: Farfesa Abubakar A. Yagawal, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga; Sheikh Muhammad Bin Uthman, Mamba na Hukumar daga Arewa maso Yamma; Dakta Tajudeen Oladejo, Mamba daga Kudu maso Yamma; Hajiya Aishat Obi Ahmed, Mamba daga Kudu maso Gabas; da kuma Dakta Mustapha Mohammed Ali, Sakataren hukumar.
An ɗora wa tawagar alhakin kammala dukkan shirye-shiryen masauki tare da gabatar da cikakken rahoto ga hukumar nan take bayan kammala aikinsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman zai cigaba da kasancewa a Nijeriya domin karɓar Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Tawfiq Al-Rabiah, wanda ake sa ran zai kawo ziyara ƙasar nan a cikin wannan wata.
