
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gidauniyar Masana’antar Kannywood, ‘Kannywood Foundation’, ta zaɓi sababbin jagorori domin gudanar da harkokinta.
An gudanar da zaɓen ne a ranar Lahadi, 1 ga Fabrairu, a ofishin gidauniyar da ke Kano, bayan ƙarewar wa’adin tsofaffin shugabannin ƙungiyar.
A sanarwar da Daraktan yaɗa labaranta, Yakubu Liman ya fitar, ya ce Khalid Musa ne aka zaɓa a matsayin Shugaba, yayin da Auwalu Isma’il Marshall ya zama Mataimakin Shugaba, sai Kabiru Maikaba a matsayin Sakatare.
Sauran shugabannin sun hada da Bala Anas Babinlata a matsayin Daraktan Ayyuka, Yakubu Liman a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a.
Shehu S. Bello a matsayin Mai Binciken Kudi, da Adamu Mohammed a matsayin Ma’aji, da kuma Ahmed Alkanawi a matsayin Daraktan cinikayya.
Gidauniyar Kannywood Foundation, ƙungiya ce ta jin kai da ke da rajista da Hukumar CAC.
Manufar gidauniyar shine bayar da gudummawa ga al’umma, tare da samar da jagoranci na gari na fada a ji, a masana’antar.
Gidauniyar na Gudanar da ayyukanta tare da hadin gwiwar sauran dattawa da Kuma jiga-jigan masana’antar fina-finan Kannywood.
