Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani sabon bincike na duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar ya nuna cewa kusan mutum huɗu cikin goma da ake kamuwa da cutar kansa a duniya za a iya kare su ta hanyar sauya halayya, ɗaukar ingantattun manufofi da kuma ƙarfafa matakan kiwon lafiya.
Rahoton, wanda aka fitar domin bikin Ranar Cutar Kansa ta Duniya da ake gudanarwa a ranar 4 ga Fabrairu, ya samo asali ne daga wani bincike da mujallar Nature Medicine ta wallafa. Binciken ya nazarci bayanai daga ƙasashe 185 da kuma nau’o’in cutar kansa 36.
A cewar sakamakon binciken, kimanin kashi 37 cikin ɗari na sabbin mutane miliyan 18.7 da aka gano suna ɗauke da cutar kansa a shekarar 2022 suna da alaƙa da abubuwan haɗari da za a iya sauyawa, ciki har da shan taba sigari, wasu kwayoyin cuta da kuma yanayin rayuwa marasa kyau.
Dakta Maria Neira, Darakta a WHO mai kula da bangaren Muhalli, Sauyin Yanayi da Lafiya, ta bayyana cewa hujjojin kimiyya sun riga sun tabbatar da cewa yawancin cututtukan kansa ba dole ba ne su kama mutum. Ta ce cututtukan da ke da alaƙa da taba sigari, kwayoyin cuta da kuma gurbataccen muhalli na daga cikin waɗanda za a iya rigakafinsu idan aka ɗauki matakan da suka dace.
Shan taba sigari na nan a matsayin babban abin da ke haddasa cutar kansa da za a iya kauce masa, inda yake da alhakin kusan kashi 15 cikin ɗari na sabbin masu kamuwa da cutar a duniya. Sauran manyan abubuwan haɗari sun haɗa da kwayoyin cuta irin su Human Papillomaɓirus (HPɓ) da kuma Helicobacter pylori, wadanda tare suke haddasa kusan kashi 10 cikin ɗari na sabbin cututtukan.
Dakta Elisabete Weiderpass, Darakta a Hukumar Bincike Kan Cutar Kansa ta Duniya (IARC), wacce ke ƙarƙashin WHO, ta jaddada cewa cututtukan da ke da alaƙa da taba sigari da kwayoyin cuta na ci gaba da jawo asarar rayuka masu yawa. Ta ce rigakafi ba wai abu ne mai yiyuwa kawai ba, abu ne da ya zama wajibi a ba shi fifiko.
ɗaya daga cikin fitattun misalan cutar da za a iya rigakafinta shi ne kansar mahaifa, wacce akasari kwayar HPV ce ke haddasawa. A yanzu haka akwai alluran rigakafi masu inganci da ke iya kare mata daga wannan kwayar cuta. Haka kuma cututtukan da ke da alaƙa da H. pylori za a iya rage su ta hanyar tsaftar muhalli, gwaje-gwajen lafiya da kuma magani tun da wuri.
Binciken ya kuma nuna bambance-bambance tsakanin maza da mata da kuma yankuna daban-daban na duniya. A maza, kusan kashi 45 cikin ɗari na cututtukan kansa na da alaƙa da abubuwan hasari da za a iya kaucewa, yayin da a mata adadin ya tsaya kusan kashi 30 cikin ɗari. Yankuna irin su Gabashin Asiya, Latin Amurka, Arewacin Afirka da Yammacin Asiya sun nuna bambancin yadda waɗannan abubuwan haɗari ke yaduwa, lamarin da ke nuna muhimmancin tsara matakan rigakafi bisa yanayin kowane yanki.
WHO na kira ga gwamnatoci da hukumomin lafiya a duniya da su ƙarfafa matakan da aka riga aka tabbatar suna aiki, kamar kara haraji kan taba sigari, hana shan taba a wuraren jama’a, faɗaɗa allurar rigakafin HPɓ, da kuma ɗaukar matakan rage gurbatar iska.
A ƙarshe, rahoton ya jaddada cewa duk da cewa cutar kansa na ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar al’umma a duniya, akwai damar rage yawan masu kamuwa da ita matuƙa idan aka mayar da hankali kan rigakafi, aka nuna kwarin gwiwar siyasa, tare da haɗin kan al’umma baki ɗaya.
