Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Gwamnonin Jihohi ta Arewa (NSGF) ta yi kakkausar suka kan sabbin hare-haren ta’addanci da suka janyo asarar rayuka a wasu sassan jihohin Kwara, Katsina da Benuwe, inda ta bayyana lamarin a matsayin dabbanci da kuma barazana ga zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya.
Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, yana mai nuna matuƙar baƙin ciki kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula marasa laifi.
Hakan na zuwa ne bayan rahotannin hare-hare a garuruwan Woro da Nuku a ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, inda ake zargin ‘yan ta’adda sun kai farmaki a daren Talata.
Haka kuma, an rawaito kashe aƙalla mutum 20 a garuruwan Doma A da Doma B na yankin Tafoki a ƙaramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.
A Jihar Benuwe ma, an samu irin wannan hari a garin Abande da ke yankin Mbaikyor Ward, Turan, a ƙaramar Hukumar Kwande, inda aka ce mutane da dama sun rasa rayukansu.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hare-haren a matsayin munanan ayyuka marasa tausayi, yana mai cewa ci gaba da kai farmaki kan mata, yara da tsofaffi na nuna tsananin rashin imani da kuma buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin kawo ƙarshen irin waɗannan laifuka.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, al’ummomin da abin ya shafa da kuma gwamnatocin jihohin uku, yana mai jaddada cewa rayukan ‘yan ƙasa na da matuƙar muhimmanci kuma wajibi ne a kare su.
Shugaban na NSGF ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnonin jihohin Kwara, Katsina da Benuwe wajen jajircewa duk da ƙalubalen tsaro da suke fuskanta, musamman ta fuskar tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa da kuma haɗa kai da hukumomin tsaro na tarayya.
Ya buƙaci hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri, sa ido da kuma gudanar da haɗaɗɗun ayyuka domin gano masu hannu a waɗannan hare-hare tare da gurfanar da su gaban kotu.
A cewarsa, kare rayuka da dukiyoyin jama’a nauyi ne mai tsarki da ke kan gwamnati, don haka bai kamata a bar masu aikata laifukan su tsira ba tare da fuskantar hukunci ba.
ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da haɗa kai da Gwamnatin Tarayya, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma domin magance matsalar tsaro ta hanyar haɗin gwiwa da kuma ɗaukar matakai na dogon lokaci da za su rage tushen tashe-tashen hankula.
A ƙarshe, Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya bai wa waɗanda suka jikkata lafiya, tare da kira ga ‘yan ƙasa da su kasance masu lura tare da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai a yaƙi da ta’addanci.
