Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ranar Talatar da ta gabata waɗansu mutane ɗauke da makamai kan babura da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan gyaran hali da ke garin Kangiwa da ke jihar Kebbi.
Wani mazauni garin Kangiwa Malam Yusuf Aliyu ya bayyanawa wakilin mu da cewa lokacin da mutanen suka zo sun ƙwace babur hannun wani mutum inda suka yi amfani da shi ta hanyar jingina babur ɗin jikin ƙofar shiga gidan suka cinna masa wuta ƙofar ta buɗe.
Bayan sun samu shiga gidan suka ƙona motar hukumar daga baya jami’an tsaro suka dira aka yi bata-kashi inda ‘yan bindigar suka gudu ba tare da sun ɗauki kowa ba.
Ya ƙara da cewa jim kaɗan bayan harin aka kwashe waɗanda ke tsare a gidan zuwa Birnin Kebbi.
Majiyoyi da dama sun labartawa Blueprint Manhaja da cewa ana sa ran waɗannan maharan sun zo ne bisa ga hasashen akwai mutanen su tsare da aka kama a gidan.
Garin Kangiwa inda nan ne shalkwatar ƙaramar hukumar Arewa yanzu haka tana cike da ‘yan gudun hijira da suka baro kauyukansu sanadiyyar mamayewar Lakurawa da masu garkuwa da mutane da kuma ɓarayin shanu.
