Mutum 162 aka kashe a harin Kwara – Red Cross

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta ce adadin waɗanda ’yan bindigar da suka kai hari ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara suka kashe a yanzu sun kai mutum 162.

An dai ƙaddamar da harin ne da yammacin Talata har zuwa wayewar garin Laraba a wani ƙauye da ke yammacin.

A baya, Gwamnan jihar ta Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, ya tabbatar da mutuwar mutane 75.

AbdulRazaƙ ya bayyana adadin ne a daren Laraba yayin da yake jawabi ga mazauna garin a fadar Sarkin Kaiama, inda ya ce waɗanda aka kashe “Musulmai ne na yankin da aka yi musu kisan gilla saboda kin miƙa wuya ga ’yan ta’addan da ke wa’azin wata baƙuwar aƙida.”

Ya kuma bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da gaggawar tura bataliya ta sojoji ƙarƙashin Operation Saɓannah Shield domin ƙaddamar da martani kan maharan.

Amma Red Cross a wata sanarwa ranar Laraba, ta ce, “Rahotanni sun nuna cewa adadin mutanen da aka kashe yanzu ya kai 162, yayin da bincike na ci gaba da neman ƙarin gawarwaki,” inji Babaomo Ayodeji, sakataren Red Cross na Jihar Kwara, wanda ya ƙara adadin da a baya aka ce 67 ne.

A baya, wani ɗan majalisa na yankin Kaiama, Sa’idu Baba Ahmed, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa (AFP) cewa an kirga “gawarwaki 35 zuwa 40” daga harin da aka kai da yammacin Talata.

’Yan sanda sun tabbatar da harin amma ba su bayar da adadin mutanen da suka mutu ba, yayin da gwamnatin jihar ta ɗora alhakin harin kan ƙungiyoyin ta’addanci.

Ahmed ya ce, “da dama sun tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga,” yana mai ƙara da cewa ana iya gano ƙarin gawarwaki daga baya.

Ya ce maharan sun kutsa ƙauyen Woro da misalin ƙarfe 6 na yamma, suka ƙone shaguna da fadar sarkin garin.

By ukarofi