Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a zamanin tsohon Shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka fi damun marigayin shugaba shi ne gazawarsa wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro gaba ɗaya kafin ya bar mulki a shekarar 2023.
Gambari ya yi wannan bayani ne yayin wata hira a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels, inda ya waiwayi salon mulkin Buhari, ƙalubalen da ya fuskanta da kuma haƙiƙanin yanayin tafiyar da mulki a Nijeriya.
A cewarsa, duk da nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a yaƙin da take yi da ƙungiyar Boko Haram, ci gaba da taɓarɓarewar tsaro a wasu sassan ƙasar ya ci gaba da damunsa har zuwa ƙarshen wa’adinsa.
Gambari ya nuna cewa Buhari ya ji zafi matuƙa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci suka yawaita musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Ya ce duk da ƙoƙarin da aka yi, lamarin bai samu waraka yadda aka so ba, abin da ya riƙa sanya tsohon shugaban cikin damuwa.
Ya ƙara da cewa, a farkon mulkinsa na farar hula, an samu manyan nasarori wajen kwato yankunan da Boko Haram ta mamaye a Arewa maso Gabas, tare da rage ƙarfin hare-harensu. Sai dai daga baya barazanar tsaro ta sauya salo, inda sabbin matsaloli suka kunno kai a wasu yankuna.
Dangane da raɗe-raɗin yunƙurin juyin mulki a ƙarshen gwamnatin Buhari, Gambari ya ce bai da masaniyar cewa irin wannan bayani ya taɓa isa ofishinsa. Ya bayyana cewa shugaban ƙasa na da hanyoyi da dama na samun bayanan sirri, ba wai ta hannun Shugaban Ma’aikata kaɗai ba.
Gambari ya kuma yi tsokaci kan zargin samuwar wata ‘cabal’ a fadar Buhari. A cewarsa, kowace gwamnati na da na kusa da shugaba mai tasiri, amma mutanen da ke kusa da Buhari sun san iyakokinsu. Ya ce Buhari mutum ne mai tsayayyen ra’ayi wanda ba ya bari a tilasta masa abu, lamarin da ya hana duk wani rukuni wuce gona da iri.
Game da batun naɗa magaji kafin zaɓen 2023, Gambari ya ƙaryata zargin cewa Buhari ya yi yunƙurin ɗorawa wani takamaiman mutum mulki. Ya ce Buhari ya yi imani da cewa ya kamata jam’iyya da masu kaɗa ƙuri’a su zaɓi wanda suke so, ba tare da katsalandan kai tsaye daga shugaba mai ci ba.
Yayin da yake waiwayar shekaru uku da ya shafe a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Gambari ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ba shi mamaki shi ne yadda wasu daga cikin mutanen da suka fi cin moriyar albarkatun Nijeriya su ne kuma suka fi nuna rashin kishin ƙasa.
A cewarsa, da dama na neman mulki ne amma ba su shirya yin sadaukarwar da ake buƙata domin tafiyar da mulki cikin adalci da hangen nesa na kasa baki ɗaya ba.
A ƙarshe, Gambari ya nuna cewa duk da akwai damammaki masu yawa a Nijeriya, akwai kuma ƙalubalen tsarin siyasa da na hukuma da ke sa sauyi cikin gaggawa ya zama abu mai wahala. Duk da haka, ya jaddada cewa ɗorewar dimokuraɗiyya na buƙatar shugabanci mai gaskiya, kishin ƙasa da kuma mutunta ƙa’idojin mulki.
