NYCN a Giwa ta yaba wa gwamnatin Kaduna, ta roƙi gyaran babban asibitin ƙaramar hukumar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar Matasan Nijeriya (NYCN), reshen ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna ta yaba wa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Sanata Uba Sani bisa ƙoƙarin da take yi wajen bunƙasa harkokin ci gaba da walwalar al’umma a sassa daban-daban na jihar.

Shugaban ƙungiyar na ƙaramar hukumar, Kwamared Nuhu Haruna Sani, wanda aka fi sani da Alkurkawee, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, inda ya ce matasan Giwa na jin daɗin yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da manufofin raya kasa musamman a fannin tsaro, ilimi da bunƙasa tattalin arzikin matasa.

Ya ce matasan yankin na lura da yadda gwamnatin Uba Sani ke ƙoƙarin inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da ayyukan yi da tallafa wa matasa domin su dogara da kansu, yana mai cewa irin wannan tsari na taimakawa wajen rage zaman banza da kuma inganta zaman lafiya a tsakanin matasa.

Sai dai Kwamared Alkurkawee ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara karkata hankali wajen gyaran Babban Asibitin ƙaramar Hukumar Giwa, wanda ya ce yana matuƙar buƙatar gyare-gyare da ƙarin kayan aiki domin ya dace da yawan al’ummar yankin da ke cin moriyar asibitin.

A cewarsa, asibitin na taka muhimmiyar rawa wajen kula da lafiyar al’ummar Giwa da ma maƙwabtansu, amma yana fuskantar ƙalubale na ƙarancin kayan aiki da buƙatar sabunta wasu sassa domin inganta ayyukan jinya da kula da marasa lafiya.

Ya ƙara da cewa gyaran asibitin zai taimaka wajen rage wahalar da al’umma ke sha wajen zuwa wasu garuruwa domin neman magani, tare da ƙara inganta tsarin kiwon lafiya a yankin baki ɗaya.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar NYCN reshen Giwa za ta ci gaba da ba gwamnatin jihar cikakken goyon baya tare da wayar da kan matasa kan muhimmancin zaman lafiya, haɗin kai da kuma bada gudunmawa wajen ci gaban yankin.

A ƙarshe, Kwamared Nuhu Haruna Sani Alkurkawee ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da bai wa Gwamna Uba Sani hikima da ƙarfin guiwa wajen jagorantar jihar zuwa matakin ci gaba mai ɗorewa, tare da fatan gwamnatin za ta duba roƙon da suka gabatar domin amfanin al’ummar Giwa.

By ukarofi