Nijeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka ƙasar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ministan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa BBC cewa wata ƙaramar tawagar sojojin Amurka tana aiki a cikin ƙasar.

Ya ce sojojin na Amurka za su kasance suna bayar da horo ga sojojin Nijeriya domin shiryasu wajen gudanar da ayyuka.

Ministan bai bayyana yawan sojojin ba, ko lokacin da suka isa ƙasar, ko inda aka jibge su, ko tsawon lokacin da za su zauna a Nijeriya ba.

Sojojin Amurka da na Nijeriya sun shafe shekaru masu yawa suna gudanar da bayar da horo na haɗin gwiwa, da nufin ƙarfafa ƙwarewar Nijeriya a fannin tattara bayanan sirri da yaƙi da ta’addanci.

Shugaban sojin Amurka a Afirka AFRICOM, Janar Dagɓin R. M. Anderson, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa tura sojojin Amurka zuwa Nijeriya ya kasance ne bisa buƙatar gwamnatin Nijeriya, kuma hankalinsu ya ta’allaka ne kan tallafi wajen tattara bayanan sirri.

Nijeriya ta ƙara haɗin gwiwa da Amurka ne a daidai lokacin da take fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, ciki har da hare-haren ‘yanbindiga da sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, da yaɗuwar ‘yan bindiga.

By ukarofi