Soyayyar Annabi ce ke ba ni ƙwarin gwiwar shirya mauludi duk shekara – Sunusi Dawaki

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Alhaji Sunusi Aminu Abubakar Dawaki ya bayyana cewa soyayya da ƙaunar Annabi Muhammad (SAW) ce ke ba shi ƙwarin gwiwar shirya bikin Mauludi duk shekara.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a gidansa a lokacin gudanar da Mauludin karo na biyu.

Ya ce duk wanda ya himmatu wajen hidimtawa Annabi Muhammad (SAW), Allah zai albarkaci dukiyarsa da rayuwarsa. Ya ƙara da cewa duk lokacin da ya shirya gudanar da Mauludi, Allah na buɗe masa hanyoyin samun nasara ba tare da neman tallafi daga kowa ba.

Ya yi kira ga mahalarta bikin da su yi amfani da darussan da malamai suka koyar domin inganta rayuwarsu da zamantakewarsu.

Shi ma Malam Abubakar Musa ya bayyana farin cikinsa da gudanar da bikin, yana mai cewa babu wata hidima da ta dace al’umma su yi murna da ita kamar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW). Ya yi fatan Allah ya ba su damar sake gudanar da irin wannan hidima a nan gaba.

By ukarofi