Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Nasiru Ibrahim Matage, ya bayyana shigar Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf cikin Jam’iyyar APC a matsayin babbar nasara ga jihar.
Hon. Matage ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a gidansa da ke garin Matage, bayan karɓar Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Sani Ahmad Mai Rago, wanda shi ma ya shiga jam’iyyar APC.
Ya ce dawowar gwamnan cikin APC zai ƙarfafa haɗin kai a jam’iyyar tare da buɗe ƙofofin samun ayyukan ci gaba daga gwamnatin tarayya.
Hon. Matage ya shawarci masu neman mukaman siyasa da su dakatar da maganar takara a halin yanzu, su mayar da hankali wajen tallafawa gwamnati domin samar da ci gaba mai dorewa.
Ya ƙara da cewa haɗewar jam’iyyun biyu zai ƙarfafa cigaban Kano tare da kawo zaman lafiya da haɗin kai a siyasar jihar.
