Kulafa’ur Rashidin Islamiyya ta yaye ɗalibai 167 a karo na 22

Spread the love

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Makarantar Kulafa’ur Rashidin Islamiyya da ke Hausawa Sabon Titi a Jihar Kano ta gudanar da bikin saukar karatun Alƙur’ani mai girma na dalibai 167 karo na 22, wanda aka yi a filin makarantar firamare ta Ado Gwaram.

Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban makarantar Malam Auwalu Umar Ahmad ya bayyana cewa makarantar na samun gagarumar nasara idan aka kwatanta da shekarun baya, musamman wajen yawan daliban da ke sauka duk shekara.

Sai dai ya bayyana cewa makarantar na fuskantar ƙalubale da suka haɗa da rashin isasshen wajen zama da kuma rashin wadatattun bandakuna. Ya ƙara da cewa babban ƙalubalen da suke fuskanta shi ne rashin biyan kuɗin makaranta daga wasu iyaye, wanda hakan ke jawo jinkirin biyan albashin malamai da kuma tafiyar da wasu ayyuka na makarantar.

Shugaban makarantar ya taya daliban murnar saukar karatun, tare da tunatar da su cewa sauka ba yana nufin sun gama neman ilimi ba ne, sai dai wani mataki ne na ci gaba.

Ya kuma bayyana cewa a mafi yawan lokuta ana samun mata sun fi yawa wajen saukar karatun, yana mai cewa hakan na faruwa ne saboda yadda mata ke mayar da hankali sosai wajen karatun addini.

A ƙarshe, ya yi kira ga iyaye da masu hannu da shuni da su tallafawa makarantar, musamman wajen gina sabon fili da aka bai wa makarantar tun zamanin tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.

By ukarofi