Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Masaukin baƙi na Port Golf da ake ginawa a birnin Kano ya samar da ayyukan yi ga matasa da dama, kamar yadda Fahad Muhammad, jami’in kula da ma’aikata da kayan aiki na Port Golf, ya bayyana a madadin Babban Manajan wurin, GM Oliver Jonathan.
Fahad Muhammad ya bayyana hakan ne a ranar Talata da ta gabata, inda ya ce aikin gina Port Golf ya bai wa matasa da dama damar samun aikin yi kai tsaye da kuma na wucin gadi, wanda hakan ke taimakawa wajen rage zaman banza da inganta tattalin arzikin matasa a jihar.
Ya ƙara da cewa Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido da Shaƙatawa ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Tukur Sagagi, ta yabawa wannan aiki bisa rawar da yake takawa wajen samar da ayyukan yi, kawata birni, da kuma dacewa da manufar gwamnatin jihar Kano na sabunta birnin Kano da bunkasa harkokin yawon buɗe ido.
Har ila yau, Fahad ya bayyana cewa Port Golf ba masaukin baƙi kaɗai ba ne, wuri ne da manyan makarantu, cibiyoyin ilimi da ƙungiyoyi ke amfani da shi wajen shirya tarurrukan ƙara ilimi, horo da musayar ra’ayi a fannoni daban-daban na rayuwa.
Ya bukaci al’umma da su fahimci muhimmancin masaukin baƙi irin Port Golf, yana mai cewa masaukin baƙi na da dogon tarihi a duniya, musamman wajen karɓar baƙi daga sassa daban-daban, ciki har da shugabanni, ‘yan kasuwa, malamai da sauran jama’a.
A cewarsa, irin waɗannan wurare na taimakawa wajen bunƙasa ilimi, shaƙatawa, buɗe ido da kuma inganta rayuwar al’umma, musamman a wannan zamani da duniya ke tafiya kan cigaba da haɗin kai a fannoni da dama.
