Daga RABIU SANUSI a Kano
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar Dawakin Tofa sun gudanar da taro na musamman da yammacin ranar Litinin, domin tattauna muhimman batutuwa da za su taimaka wajen bunkasa cigaba da hadin kai a karamar hukumar.
Taron wanda ya samu halartar manyan jagorori da jiga-jigan jam’iyyar daga matakai daban-daban.
Daga cikin mahalarta akwai Babban Daraktan Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Sanusi Bature D-Tofa.
Sauran wadanda suka halarta sun hada da Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Adamu Shehu Bello Danmaliki,tsohon dan takarar Majalisar Tarayya a jam’iyyar APC a zaben 2023, Injiniya Abba Ganduje da kuma dan Majalisar Jihar Kano mai wakiltar Dawakin Tofa, Alhaji Sale Marke.
Haka kuma taron ya samu halartar tsohon dan takarar Majalisar Jihar Dawakin Tofa a zaben 2023, Hon. Ahmad Muhammad (Speaker), Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Abdullahi Magaji Aliyu Kosasshe ,House Leader na Dawakin Tofa, Hon. Auwalu Dahiru Dambazau tare da sauran manyan jagororin jam’iyyar.
Masu jawabi a taron sun jaddada bukatar hadin kai, fahimtar juna da kuma tsara dabarun da za su kawo cigaba mai dorewa ga al’ummar Dawakin Tofa. A karshe, mahalarta sun yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya tabbatar da nasara da zaman lafiya a yankin.
