Hon. Jibga da Sa’in Kano sun jagoranci bikin cika shekaru 30 da kafuwar ƙaramar Hukumar Makoɗa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban ƙaramar Hukumar Makoda, Hon. Alhaji Isah Jibga, tare da Sa’in Kano kuma Hakimin Makoda, Arc. Alhaji Ali Mukhtar, sun jagoranci bikin cika shekaru 30 da kafuwar ƙaramar Hukumar Makoda, wadda aka kirkira a shekarar 1996 daga tsohuwar ƙaramar Hukumar Danbatta.

An gudanar da bikin ne a harabar fadar Masarautar Makoda a makon da ya gabata, inda manyan baki, shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, malamai da al’ummar yankin suka halarta domin tunawa da gagarumar gwagwarmayar da aka yi har aka samu kafuwar ƙaramar hukumar.

Tun da farko a jawabinsa, Hon. Alhaji Isah Jibga ya bayyana ranar a matsayin wata babbar rana ta tarihi da alfahari ga al’ummar Makoda da ma masoyansu a ko’ina suke a fadin duniya. Ya ce kafuwar ƙaramar hukumar ta kawo sauye-sauye masu ma’ana da ci gaba a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma.

Shugaban ya yi amfani da damar wajen yi wa rayukan waɗanda suka yi gwagwarmayar neman kafuwar Makoda addu’a, yana mai jaddada cewa ba za a manta da irin gudunmawar da suka bayar ba. A yayin bikin, an raba atamfofi masu daraja ga mata sama da 2,000, a matsayin tallafi da kuma tunawa da ranar.

Hon. Jibga ya kuma bayyana muhimman nasarorin da ƙaramar hukumar ta samu a baya da kuma a wannan zamani na mulkinsa, ciki har da samar da ruwan sha, gyaran hanyoyi, sabunta sakatariyar ƙaramar hukumar, samar da kayan aiki a bangaren lafiya, da kuma inganta walwalar ma’aikata da al’umma gaba ɗaya.

Shi ma a jawabinsa, Sa’in Kano kuma Hakimin Makoda, Arc. Alhaji Ali Mukhtar, ya bayyana bikin a matsayin ranar ƙara ɗaurewar zumunci, kishin ƙasa, kishin ilimi da kuma ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin al’umma. Ya jaddada cewa adalci da gujewa zalunci su ne ginshiƙan samar da zaman lafiya a kowace al’umma.

A nasa jawabin, Alhaji Lawan Shehu Makoda, wanda shi ne shugaban kwamitin bikin kuma mataimakin sakataren gwagwarmayar neman kafuwar ƙaramar hukumar a shekarar 1996, ya bayyana irin gagarumin ci gaban da Makoda ta samu musamman a fannin ilimi. Ya ce a lokacin kafuwar ƙaramar hukumar akwai makarantar sakandare guda ɗaya kacal, amma yanzu sun haura takwas, yayin da makarantun firamare suka kai sama da 70.

Sai dai ya zayyana wasu manyan ƙalubale da har yanzu Makoda ke fuskanta tsawon shekaru 30, ciki har da rashin babban asibiti, da kuma rashin makarantar kwana ga maza da mata, wanda ya ce akwai buƙatar gaggawar daukar mataki daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Shi ma Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Ali Haruna Makoda, ya bayyana bikin a matsayin darasi mai girma, inda ya bukaci al’umma da kowa ya bayar da tasa gudunmawa wajen ci gaban yankinsa, yana mai cewa yawanci masu fafutukar ci gaba ba su ne kaɗai ke cin moriyar nasarorin ba, don haka suna buƙatar addu’a da girmamawa.

A ƙarshe, Malam Ado Shitu Dunawa, wanda shi ne ya fara rubuta takardun neman kafuwar Makoda tare da kasancewa sakataren fafutukar, ya bayyana asalin Makoda da tarihinta, yana mai cewa yankin ya samo sunansa ne daga sana’ar nika dutse da mata ke yi tun zamanin da. Shi ma Muhammad Haladu Galadima na daga cikin masu jawabi a bikin, inda ya yabawa shugabanni da al’ummar Makoda bisa haɗin kai da jajircewa.

By ukarofi