Kante ya koma Fenerbahce daga Al-Ittihad

Spread the love

Fenerbahce ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan tawagar Faransa, N’Golo Kante, daga Al-Ittihad mai buga babbar gasar tamaula ta Saudiyya.

A ranar Talata, shirin ɗan wasan Faransan na komawa Turkiyya ya kusan rushewa, bayan Fenerbahce ta fitar da sanarwa tana zargin Al-Ittihad da haddasa kawo cikas a cinikin.

Fenerbahce ta ce Al-Ittihad ta kasa cika takardun da ake buƙata don kammala kulla yarjejeniya daga ciki ɗan wasan tawagar Moroko, Youssef En-Nesyri ya koma Al-Ittihad.

Sai dai a ranar Laraba, Fenerbahce ta tabbatar da cewa an warware matsalar da ke tsakaninsu, kuma Kante tsohon ɗan wasan Chelsea ya koma Turkiya, bayan shafe shekara biyu da rabi a Saudiyya.

Kante, mai shekaru 34, ya koma Al-Ittihad daga Chelsea a shekarar 2023, bayan lashe Gasar Zakarun Turai (Champions League) da Premier League da Europa League da FA Cup.

Ya koma Chelsea ne daga Leicester City a shekarar 2016, bayan da ya bayar da gudunmuwar da Leicester ta lashe kofin Premier League.

En-Nesyri, mai shekaru 28, zai maye gurbin tsohon ɗan wasan Real Madrid, Karim Benzema, wanda ya koma Al-Hilal a makon nan.

By ukarofi