Jurrien Timber na ganin cewa lashe kofin Carabao Cup na iya zama wata hanya ta buɗe ƙofofin samun manyan nasarori ga Arsenal a wannan kakar ta bana.
Kungiyar da Mikel Arteta ke jagoranta tana daf da kawo ƙarshen shekara shida ba tare da kofi ba, bayan da ta doke Chelsea a filin Emirates 1-0, kenan ta kai wasan ƙarshe da cin 4-2 gida da waje.
Arsenal ta kare a mataki na biyu sau uku a teburin Premier League, sai dai a bana tana kan teburi da tazarar maki shida tsakani da Manchester City ta biyu – kuma ita ce ta ja ragamar teburin Champions League da lashe dukkan karawa takwas gida da waje.
Haka kuma, Arsenal za ta karɓi baƙuncin Wigan Athletic mai buga League One a zagaye na huɗu na FA Cup.
