Gwamnatin Tarayya ta bai wa ’yan Nijeriya wa’adi kan sabuwar dokar haraji

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fadar Shugaban ƙasa ta yi kira ga dukkan ’yan Nijeriya, ɗaiɗaikun mutane da kuma masu ɗaukar ma’aikata, da su tabbatar sun cika ƙa’idojin doka ta hanyar miƙa takardun bayanan harajinsu na shekara kafin ko a ranar 31 ga Maris, tana mai gargaɗin cewa rashin bin doka a fannin haraji na ci gaba da zama babbar matsala ga tsarin tattalin arzikin ƙasar.

Shugaban Kwamitin Shugaban ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan yayin wani taron yanar gizo da aka shirya domin jami’an kula da albarkatun ma’aikata, masu kula da albashi, manyan jami’an kuɗi da kuma kwararrun masu lura da haraji, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Kuɗaɗen Shiga ta ƙasa, wato Joint Revenue Board.

Taron ya mayar da hankali ne kan inganta bin dokokin haraji da kuma fayyace nauyin da ke kan ’yan ƙasa a ƙarƙashin sabbin tsare-tsaren haraji da ake aiwatarwa.

Oyedele ya jaddada cewa doka ta wajabta wa masu ɗaukar ma’aikata su gabatar da rahoton haraji na shekara dangane da ma’aikatansu, ciki har da hasashen albashin da za su biya da kuma harajin da ya rataya a kansa.

Ya ce, da dama daga cikin kamfanoni sun riga sun yi hakan, amma waɗanda ba su kammala ba na da ’yan kwanaki kaɗan kacal su cika wannan sharaɗi kafin wa’adin ya cika.

Baya ga masu ɗaukar ma’aikata, Oyedele ya bayyana cewa wajibi ne ga kowane mutum mai samun kuɗin shiga ya miƙa bayanan harajinsa na ƙashin kai, yana mai cewa matakin bin doka a faɗin ƙasar na da matuƙar rauni.

A cewarsa, ko a jihohin da ake ganin sun fi ci gaba, ba za a iya cewa ko kashi biyar cikin ɗari na masu biyan haraji ne ke cika takardunsu yadda ya kamata ba, alamar cewa akwai babbar giɓin fahimta da kuma rashin kulawa da wannan wajibci na doka.

Ya kuma bayyana cewa ma’aikata ba za su ɗauka cewa an gama da nauyin harajinsu ba muddin an cire musu harajin PAYE daga albashi.

A cewarsa, ko a tsohon tsarin haraji ko a sabon tsarin da ake aiwatarwa, kowane ma’aikaci har yanzu na da alhakin miƙa nasa bayanin haraji na ƙashin kansa.

Oyedele ya ƙara da cewa wannan sharaɗi ya shafi kowa, har ma da masu ƙaramin ƙarfi, domin cika takardun haraji wajibi ne na doka ba tare da la’akari da yawan kuɗin shiga ba.

Ya bayyana cewa hukumomin haraji na aiki tare domin sauƙaƙa tsarin cika takardun, ta yadda mutane za su fi samun sauƙin bin doka ba tare da tangarɗa ba.

Haka kuma ya sanar da cewa a ƙarƙashin sabbin dokokin haraji, kamfanonin da ke cin gajiyar rangwamen haraji ko wasu tallafe-tallafe na musamman wajibi ne su bayyana hakan a fili yayin da suke miƙa takardunsu.

A cewarsa, wannan sabon tsari na bayyanawa zai ƙara inganta gaskiya da riƙon amana a harkokin haraji, tare da taimakawa gwamnati wajen faɗaɗa tushen kuɗaɗen shiga da rage dogaro da bashin cikin gida da na waje domin tafiyar da ayyuka.

Daga ƙarshe, Oyedele ya buƙaci ’yan Nijeriya su ɗauki biyan haraji da cika takardu ba kawai a matsayin wajibcin doka ba, har ma a matsayin gudunmawa ta ƙasa wajen gina tattalin arziki mai ɗorewa da ci gaban al’umma baki ɗaya.

By ukarofi